Kotu Ta Wanke Tsohon Shugaban EFCC Magu Daga Zargin Sace Kudin Kasa

Kotu Ta Wanke Tsohon Shugaban EFCC Magu Daga Zargin Sace Kudin Kasa

  • An wanke tsohon shugaban hukumar dakile yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu daga zargin da ake masa na aikata zambar kudade
  • Ana zargin Ibrahim Magu ne da cin kudaden kasa tun shekarar da ta gabata, lamarin da ya kawo cece-kuce a Najeriya
  • Ana yawan samun zarge-zargen rashawa daga manyan jami'an gwamnati, musamman kan lamurran da suka shafi kudi a Najeriya

FCT, Abuja - Wata kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta wanke tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu daga zargin da ake masa na yin awon gaba da wasu kudade.

Mai shari'a Yusuf Halilu ne ya yanke hukuncin a jiya Talata 4 ga watan Oktoba, inda yace hujjojin da fasto Emmanuel Omale da matarsa suka gabatar na cewa Magu ya yi zambar N573m na cike kura-kurai.

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a Sun Maka IGP da CMD Kotu, Sun Bukaci Alkali Ya Jefa su Kurkuku

An wanke Ibrahim Magu na EFCC daga zargin sace kudin kasa
Kotu Ta Wanke Tsohon Shugaban EFCC Magu Daga Zargin Sace Kudin Kasa | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, ma'auratan biyu sun shigar da kara cewa, Magu ya umarce su da hada baki wajen sace kudade masu yawa.

A binciken da fadar shugaban kasa ta gabatar karkashin mai shari'a Isa Salami ta gano cewa, Magu ya tura kudaden da suka kai N573m zuwa asusun bankin cocin Omale.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton da aka tattara kan kudin da Magu aka ce ya sata

Rahoto ya bayyana cewa, an gano an siyawa tsohon shugaban na EFCC a kasar Dubai, rahoton jaridar Punch.

Amma da yake gabatar da hukunci, mai shari'a Halilu ya ce hujjojin da aka gabatar sun nuna an samu kuskuren bayanai daga asusun bankin cocin Omale.

Mai shari'a ya ce, kuma da tarin kura-kuran aka mikawa hukumar bincike rahoton hujjojin, wannan yasa aka warware batun cewa Magu ya saci kudi.

Kara karanta wannan

Lambar Girma: Yadda Ake ta Surutu Yayin da Manyan Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi

Ya kuma bayyana cewa, bayanan da faston ya gabatar sun ce, an samu kuskuren shigar kudi ne zuwa asusun cocin.

Hakazalika, ya ce daga baya banki ya tabbatar da inganta bayanansa tare da bayyana inda aka samu matsala a asusun cocin Omale.

Hukumar ’Yan Sanda Ta Kori Manyan Jami’ai 7, Ta Ragewa 10 Matsayi

A wani labarin na daban, hukumar aikin dan sanda ta PSC ta sanar da korar wasu jami'ai bakwai saboda halin rashin da'a a ranar Talata 4 ga watan Oktoba.

Haka nan, hukumar ta kuma amince da rage girman wasu manyan jami'ai 10 nata, inji rahoton Daily Trust.

Wannan mataki na zuwa ne a ci gaba da zama na 15 na hukunci da da sauraran koke da hukumar ke yi a kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.