Da Duminsa: FG Zata Gabatar da Shaidar Rijista ga CONUA don Ganin Bayan ASUU

Da Duminsa: FG Zata Gabatar da Shaidar Rijista ga CONUA don Ganin Bayan ASUU

  • Gwamnatin tarayya ta fara bin hanyoyin kwace rijistar kungiyar Malamai masu koyarwa a jami’o’i, ASUU
  • Kamar yadda jami’i daga ma’aikatar kwadago ya bayyana, a yau Dr Ngige zai mika shaidar rijista ga CONUA
  • CONUA wata tsagin ASUU ce wacce hakan zata tabbatar da murkushe kungiyar ASUU da kawo karshen yajin aikin da yaki karewa

Gwamnatin tarayya ta fara bin Ladin an kwace rijistar Kungiyar Malamai ta Jami’o’i, ASUU.

Daily Trust ta gano cewa, Congress of Nigerian University Academics, CONUA, tsaro ASUU an yi mata rijista a matsayin kungiya.

Wata majiya daga ma’aikatar Kwadago da aikin yi ta sirranta da Daily Trust a ranar Talata inda tace Ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige, zai gabatar da shaidar rijistar sabuwar kungiyar kafin wunin yau ya kare.

Jami’in yayi bayanin cewa, wannan yunkurin na gwamnati yana daga cikin hanyoyin da ta fada na kwace rijistar ASUU, da zummar dakile tsabar yajin aikinsu da yayi sanadiyyar garkame jami’o’in gwamnati na tsawon wata bakwai.

Kara karanta wannan

Ku mutunta umarnin kotu ku janye yajin aiki, gwamnatin Buhari ga ASUU

“A madadin gwamnatin tarayya, Ministan Kwadago zai gabata da shaidar rijista ga tsagin ASUU mai suna CONUA. Da hakan ne ta yuwu a kawo karshen ASUU a jam’o’i."

- Majiyar tace.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Trust ta rahoto yadda a watan Satumba gwamnati ta fara barazanar kwace rijistar ASUUa matsayin kungiya kan zarginta da gazawa wurin mika rahoton yadda take kashe kudinta na tsawon shekaru biyar da suka gabata.

FG Zata Janye Rijistar Kungiyar ASUU, Ta Bayyana Dalilinta

A wani labari na daban, alamu sun bayyana a ranar Laraba cewa gwamnatin tarayya na iya janye rijistar kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, a matsayin kungiyar kwadago sakamakon gazawarta na gabatar da rahotonta na tantancewa kamar yadda doka ta tanada a shekaru biyar da suka gabata.

Tuni dai aka bayyana cewa, magatakardar kungiyar kwadagon ya rubutawa kungiyar takardar tuhuma kan dalilin da ya sa ba za a janye satifiket din rijistar ta ba saboda taka doka, Vanguard ta rahoto.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da malaman jami’o’i a fannin likitanci suka nemi ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta Najeriya da ta yi musu rijista a matsayin kungiyar kwadago ta daban a karkashin kungiyar Nigerian Association of Medical and Dental Academics, NAMDA.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng