Karin Bayani: Buhari Ya Halarci Taron Kasa Kan Rage Cin Hanci A Hukumomin Gwamnati, Ya Zargi ASUU Da Rashawa

Karin Bayani: Buhari Ya Halarci Taron Kasa Kan Rage Cin Hanci A Hukumomin Gwamnati, Ya Zargi ASUU Da Rashawa

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron kasa kan rage cin hanci a hukumomin gwamnati da aka gudanar a Abuja
  • Manyan manyan yan Najeriya sun samu halartar taron ciki har da tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, Shugaban ICPC, Bolaji Owasanoye
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma yi zargin kungiyar malaman jami'o'in Najeriya, ASUU, da rashawa

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari da shugaban hukumar yaki da rashawa da abubuwa masu alaka da rashawa, Farfesa Bolaji Owasanoye a halin yanzu suna halartan taron kawar da rashawa a aikin gwamnati da ake yi a gidan gwamnati.

Taken taron na bana shine "Rashawa Da Bangaren Ilimi'.

Shugaba Buhari
Buhari, Jega Da Wasu Sun Jiga-Jigan Yan Najeriya Na Halartar Taron Yaki Da Rashawa A Abuja. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, da tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na kasa, INEC, Attahiru Jega sun halarci taron, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hukumar 'yan sanda ta kori wasu manyan jami'anta 7, ta ragewa 10 girma

Saura da suke wurin taron akwai masu sarautan gargajiya da malaman addini da yan yi wa kasa hidima, daliban sakandare da yan jarida.

Buhari ya zargin ASUU da rashawa

Yayin bude taron da Hukumar yaki da rashawa ta ICPC, ofishin sakataren gwamnatin tarayya, OSGF, da hukumar JAMB suka shirya, Buhari ya ce ASUU na da hannu a rashawar da ke faruwa a makarantun gaba da sakandare.

Ya ce rashawar na cigaba da dakile kudaden da aka kashewa a bangaren ilimi, yayin da masu suka ba su magana kan hakan sai dai batun kudaden da ya kamata a rika ware wa bangaren, ya yi kira a sake duba tsarin kudaden da aka kashewa, Daily Trust ta rahoto.

Shugaban kasar ya sha yin kira ga malaman jami'o'in su hakura su koma aji tun bayan da suka fara yajin aiki na tsawon watanni a kalla shida amma hakan ya ci tura.

Kara karanta wannan

Shugaba Muhammadu Buhari Ya yi Sabon Nadin Mukami a Gwamnatin Tarayya

Malaman sun fara yajin aikin ne tun a ranar 14 ga watan Fabrairu kan batutuwa da suka shafi allawus-allawus dinsu da albashi da wasu abubuwan

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

A wani rahoton, tsohuwar 'Yar A mutum Buhari, Naja’atu Mohammed, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Afrilu ya yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164