Shugaba Buhari Zai Karrama Gwamna Zulum Da Wata Lambar Yabo Mai Girma

Shugaba Buhari Zai Karrama Gwamna Zulum Da Wata Lambar Yabo Mai Girma

  • Shugaban ƙasa, Alhaji Muhammadu Buhari, zai karrama gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum ranar 11 ga watan Oktoba
  • A wata wasiƙa da ministan ayyuka na musamman, George Akume, ya aike wa gwamnan, yace Buhari ya amince da girmama Zulum da CON
  • Gwamna Zulum ya karɓi lambar yabo da dama daga manyan jaridu da ƙungiyoyi, ciki har da na jami'ar Ibadan

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da karrama gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum da lambar girma ta ƙasa CON "Commander of the Order of the Niger."

Ministan ayyuka na musamman da harkokin cuɗanya da gwamnati, Sanata George Akume, shi ne ya sanar da haka a wata wasika da ya aike wa Zulum, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Zulum tare da shugaba Buhari.
Shugaba Buhari Zai Karrama Gwamna Zulum Da Wata Lambar Yabo Mai Girma Hoto: BuhariSallau
Asali: Facebook

A wasiƙar, Ministan yace:

"Ina mai sanar maka da cewa shugaban tarayyan Najeriya, Muhammadu Buhari, GCFR, ya amince zai karramaka da lambar yabo ta ƙasa watau CON."

Kara karanta wannan

2023: Ƙarin Matsala ga Atiku, Wani Shugaba a PDP da Ɗaruruwan Mambobi Sun Sauya Sheka Zuwa APC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanata Akume, a wasiƙar mai ɗauke ɗa kwanan watan 19 ga watan Satumba, 2022 da lambar asali FMSDIGA/NHA/001k/T/90 yace za'a gudanar da bikin ba da lambar ƙasan da safiyar Talata, 11 ga watan Octoba, 2022 a cibiyar ICC Abuja.

Lambar girmamawa ta ƙasa ita ce mafi kololuwar karrama wa da shugabannin mafi yawan ƙasashe ke baiwa 'yan ƙasa, waɗanda suka ba da gudummuwa gagara misali wajen yi wa ƙasa hidima.

Bazoum ya karrama Zulum

A ranar Talata, 28 ga watan Agusta, 2021 shugaban jamhuriyar Nijar, Muhammad Bazoum, ya karrama Zulum da wata lambar girma mai suna, "“de Grand Officer Dans I`Ordre."

Karammawar ta shugaban Nijar na da daraja dai-dai da 'GCON' a matakan girmama wa na Najeriya.

Gwamna Zulum ya karɓi lambar yabo sama da 20 kuma mafi yawansu manyan jaridu a Najeriya da kuma fitattun ƙungiyoyi da makarantu suka karrama shi, daga ciki har da karramawar da Jami'ar Ibadan ta masa.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu, Obi Ko Kwankwaso? Namadi Sambo Ya Faɗi Wanda Ya Dace Ya Gaji Buhari a 2023

A wani labarin kuma Buhari Zai Karrama Sarkin Kano, Sarkin Zazzau Da Wasu Sarakuna 18 Da Lambar Girma Ta Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karrama mutane fiye da 400 da lambar girmamawa ta kasa na 2022.

Daga cikin wadanda za a girmama akwai manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, manyan masu fada aji da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262