Rikicin PDP: Atiku yayi alkwarin marawa Wike baya a shekarar 2027

Rikicin PDP: Atiku yayi alkwarin marawa Wike baya a shekarar 2027

  • Wike yasha alwashi marawa duk wanda yai nasara baya
  • Amma duk da hakan an ga wiken da wasu jiga-jigan jam'iyyar ficewa daga tawagar yakin neman zaben sa
  • A kwanan nan rikici a dabaibaye Jam'iyyar.

‘Yan Jam'iya yan takara da magoya bayansu dai sun shiga tsaka mai wuya tun bayan Da dan takarar Jam'iyyar PDP ya Zabi Ifenyi Okowa watan Yuni lokacin da gwamnan jihar Delta a matsayin mataimakin shugaban kasa wanda ya yi watsi da Wike.

Tun bayan lokacin kananun matsaltsalu na ta bayyana wanda har suka haifar da manya matsalar da ta bayyana. Hakan yasa akai ta Yunkurin sulhun ta su duk da ba haifar da wani sakamako mai kyau ba.

Har ma Atiku ya yanke shawarar yin watsi da Wike, kuma ya ci gaba da yakin neman zabensa yayin da Gwamnan Jihar Ribas da magoya bayansa suka yi barazanar cewa baza mu marawa Atiku baya ba a yakin Neman Zabe

Kara karanta wannan

Ba Ta Bani Hakki Na: Miji Zai Saki Uwar 'Ya'yansa 8 Saboda Ta Daina Kwana Tare Dashi A Daki

Biyar daga cikin tsoffin gwamnonin da aka zaba a tawagar yakin neman zabe su fice daga tawagar tare da marawa wike baya. Baya ga wasu jigagan jam'iyyar da suka ki mara masa baya.

Sai dai wani sabon yunkurin da ya hada su a ranar Alhamis din nan. Atiku ya roki Wike da ya mara masa baya tare da shigawa tawagar yakin neman zaben nasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyoyin da ke kusa da taron sun ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya yi tayin marawa Wike baya a zaben shugaban kasa a 2027 muddin ya goya masa baya.

Wike dai yana zargin rashin adalci da shugaban jam'iyyabyayi musu shi da masu mara masa baya.

Hakazalika majiyoyin sun shaidawa manema labarai cewa Wike ba yi wata murna da jindadin tayin mara baya a 2027 ba duba da irin alkawarin da Atiku ya yi wa kabilar Igbo yayin ganawarsa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a Enugu a farkon makon nan.

Kara karanta wannan

2023: Nan Babu Dadewa Wike da Tawagarsa Zasu Koma Wurin Tinubu, 'Dan APC Yayi Hasashe

Wani Bincike ya nuna Atiku ya gana da Wike a gidansa dake rukunin gidajen gwamnoni da ke yankin Asokoro a Abuja.

Wata majiya da ta boye sonanta ta ce:

“Haka kuma, Atiku ya mika takardun bayanan kamfe ga Wike tare tare bashi yan itaciya na Zaitun. Ya roki gwamnan da ya kalli babban kalubalen lashe zaben lashe zaben 2023.
“Ya roki Wike da yayi nasara shawo kan yan tawagarsa don shiga tawagar yakin neman zaben PDP.
"Atiku ya yi alkawarin yin adalci ga dukkan 'ya'yan PDP duk da bambance-bambancen da aka samu a makonnin da suka gabata wanda sakamakon zaben fidda gwani na jam'iyyar ya haifar."

goyon bayan Wike a 2027 idan ya ba shi goyon bayan da ya dace a yakin neman zaben da ke gudana.ewa zai je ya tuntubi tawagarsa kafin yanke hukunchi"

Wata majiya a tsagin Wike ta ce:

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Na Fama Da Matsanancin Yunwa Ta Yadda Basa La'akari Da Addinansu A Zaben 2023 - Keyamo

“Gwamnan bai ji dadin tayin mara baya na zaben 2027 ba saboda ya yi wa Igbo irin wannan tayi a Enugu kwanakin baya.
“Babban kalubalen da Wike ke ganin Atiku bai magance shi ba shine rashin amincewa da tsagin mu. Sannan tsaginmu mu na da ra'ayin cewa Atiku yana tafiya a kan wata yarjejeniya ko batu saboda matsin lamba nan da can.
“Wannan rikicin ba zai kai wannan matakin ba idan Atiku ya rike amanar da tattaunawar da mukai dashi a Landan da yarjejeniyar da ba'a rubuta ba"
"Tsaginmu za ta dau matsaya kan marawa Atiku baya ko a'a"

Asali: Legit.ng

Online view pixel