Yayinda RIkici Ya Karade Jam'iyyarsa, Shugaban PDP, Iyorchia Ayu, Ya Dawo Najeriya
- Ana tsaka da zarginsa da handame wasu makudan kudin jam'iyya, Ayu ya dawo gida Najeriya
- Rikicin da ya 'dai'daita jam'yyar adawa ta PD ya dau sabon salo da yammacin Alhamis yayinda shugabanni suka fara mayar da kudaden da aka tura musu
- Gwamna Nyesom Wike a makon da ya gabata ya bayyana cewa shugaban PDP ya karbi cin hancin N1bn
FCT, Abuja - Shugaban uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Dr. Iyorchia Ayu, ya dawo Najeriya bayan makonni biyu da ya kwashe a nahiyar Turai.
Daily Trust ta ruwaito cewa jirign da Ayu ya shiga ya dira babbar tashar jirgin Nnamdi Azikwe ne misain karfe 7 na yammacin Juma'a, 30 ga watan Satumba, 2022.
Ayu Ya dawo Najeriya ne yayinda jam'iyyarsa ke gab da rabewa biyu kuma wasu mambobin kwamitin gudanarwarsa na zarginsa da raba musu kudin cin hanci.
Shugabannin jam'iyyar shida sun mayar da makudan miliyoyin da Shugaban jam'iyyar ya tura musu asusun bankinsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daga cikinsu akwai Mataimakin uwa jam'iyyar na Kudu, Taofeeq Arapaja, Mataimakin jam'iyya na yankin Kudu maso yamma, Olasoji Adagundo, Mataimakin jam'iyya na yankin Kudu maso kudu, Dan Orbihda Shugabar Matan jam'iyyar, Prof. Stella Affah-Attoe.
A wasikar da suka aikewa shugaban uwar jam'iyyar, Iyorchia Ayu, sun bayyana cewa basu san dalilin biyansu wadannan kudade ba.
Sunce kudin da aka ce musu na kudin haya ne ana tuhumarsu da cewa na toshiyar baki ne don su goyi bayan Shugaban jam'iyyar kan tunbukesa da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ke yi.
Rikici Ya Barke a Kwamitin NWC Na Jam’iyyar PDP Akan Kudi Naira Biliyan 10 Na Fom Din Takara
Mun kawo muku cewa rikici ya sake barkewa a jam'iyyar kan yadda aka kashe kudin foma-foman da PDP ta siyar gabanin zabukan fidda gwani.
Kwamitin ayyukan PDP ne ke tado da wannan batu na sanin bahasin kashe Naira biliyan 10, inji rahoton The Nation.
Wasu mabobin NWC sun nuna damuwa game da yadda kudin ya zaftare daga Naira biliyan 10 zuwa Naira biliyan 1.
Batutuwan da ke fitowa sun ce, PDP na shirin ba dukkan mamban NWC da ke neman bahasi N28m domin rufe musu baki kan tado da sabon rikici a jam'iyyar.
Asali: Legit.ng