'Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojojin Najeriya Kwantan Ɓauna, Sun Kashe Wasu a Zamfara
- Miyagun yan bindiga sun kashe sojin Najeriya yayin da suka musu kwantan ɓauna a yankin Kauran Namoda, jihar Zamfara
- Wani mazaunin yankin yace lamarin ya faru ne yayin da sojojin ke kan hanyar kai ɗauki bayan samun bayanan sirri
- Har yanzun hukumar soji da hukumar 'yan sanda ba su ce komai ba game da sabon harin
Zamfara - Sojoji uku sun rasa rayukansu yayin da wani ɗaya ya jikkata bayan wasu tsagerun 'yan bindiga sun musu kwantan ɓauna a kusa da ƙauyen Dolen-Kaura, ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda, jihar Zamfara.
Wani ɗan asalin yankin wanda ya roki kar a saka sunansa, ya shaida wa jaridar Punch cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba da daddare lokacin da yan ta'adda suka mamayi motar sojojin da ke bakin aiki.
A cewarsa, sojojin sun samu bayanin cewa wasu 'yan ta'adda sun shirya zasu kai hari ƙauyen Kada-Mutsa, ƙaramar hukumar Zurmi, bisa haka aka tura su daƙile kai harin, jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.
Bisa rashin sa'a, yan bindigan dajin suka sami labarin cewa sojoji na kan hanya zasu kai musu samame, "Nan yan bindigan suka yi kwantan ɓauna suka buɗe wa motar da ta ɗakko sojojin wuta, uku suka mutu ɗaya ya ji rauni," inji shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutumin ya faɗi sunan shugaban tawagar sojojin da, "Mejo Emos," inda ya bayyana shi da gwarzon jami'in soja da bai san tsoro ba.
"Gwarzon soja ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin kare rayukan mutane a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda. Mamacin ya kasance ko da yaushe a shirye idan aka yi kiran gaggawa 'yan bindiga sun kai hari."
"Mutuwara babban rashi ne ba wai ga mazauna Ƙauran Namoda da kewaye kaɗai ba, baki ɗaya al'ummar jiha sun yi rashi."
Har yanzu da muke kawo muku wannan rahoton babu wata sanarwa daga hukumar soji ko ta 'yan sanda game da lamarin da ya auku.
Yan bindiga sun kashe ɗan sanda
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kashe Dan Sanda Da Wasu 3, Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Masu Yawan Gaske A Jihohin Arewa 2
Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane sun sun kai munanan hare-hare jihohin Katsina da Kaduna.
A Kaduna maharan sun kashe mutane uku sannan suka yi awon gaba da wasu mutum 22 a garuruwan Birnin Gwari.
Asali: Legit.ng