Bauchi: Hotunan Makarantar Sakandare Mai Dalibai 1500 amma Babu Bencinan Zama da Bandaki
- Hotunan kwalejin koyar da addinin Islama ta Yakubu Bauchi dake karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi sun ba jama'a mamaki
- Lalatattu da tabarbararrun ajujuwan daliban sun nun yadda dalibai ke zama a kasa ana karatu babu ko alamar bencin zama balle na rubutu
- Ba nan lamarin ya tsaya ba, babu ko bandaki daya a fadin makarantar sakandaren mai dalibai sama da 1500
Toro, Bauchi - Hotunan wata makarantar sakandare a jihar Bauchi mai suna Kwalejin koyar da ilimin addinin Islama ta Yakubun Bauchi mai dalibai sama da 1500 amma babu bencina ko bandaki ya ba jama'a mamaki.
Wannan an tattaro shi sakamakon wallafar da TrackaNG, wata kungiyar taimakon kai da kai dake haskowa tare da bankado yadda aka aiwatar da manyan ayyukan gwamnati.
Kamar yadda TrackaNG ta saba, tana nemowa tare da nunawa 'yan kasa yadda ayyukan ko gudana ko akasin hakan kuma sun yi wannan fallasar ne a ranar Talata.
Kungiyar ta wallafa hotunan lalatattun gini da ajujuwan makaranta a shafinsa na soshiyal midiya inda tayi kira ga gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, da ya gyara makarantar dake karamar hukumar Toro ta jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
TrackaNG tace:
"Dukkan ajujuwan sun tabarbare tare da lalacewa, daya kadai ya rage. A 2021, makarantar ta samu N20 miliyan daga gwamnati don tayi gyara kuma sun gyara a ajujuwa biyu amma babu bencina.
"Makarantar tana da sama da dalibai 1500 kuma babu wani benci ko kayan karatu. Babu bandaki a makarantar. Gwamnan Bauchi ka kawo dauki gtare da gyara kwalejin karatun Islama ta Yakubu Bauchi."
Hotuna: Wata makarantar firamare da dalibai ke daukar darasi a ajin bukka, gindin bishiya kuma shine ofishin hedimasta
A wani labari na daban, wata makarantar firamare a jihar Cross River ta zamo abar kwatance a wajen wata kungiya, bayan an gano cewa daliban makarantar suna daukar karatu a ajin bukka.
Lydia Yegraowo Okache da Godwin Onah suna daga cikin 'yan wannan kungiyar, kuma sune suka sanya hoton wannan makaranta bayan sunje sun kai musu gudummawar litattafan karatu.
Makarantar mai suna 'Community Primary School' dake kauyen Akpanda Itega-Egbudu dake karamar hukumar Yala cikin jihar ta Cross River, ita ce makarantar da ofishin shugaban makarantar yake a karkashin bishiya, sannan daliban ana koya musu darasi a ajin bukka.
Asali: Legit.ng