Hotuna: Wata makarantar firamare da dalibai ke daukar darasi a ajin bukka, gindin bishiya kuma shine ofishin hedimasta
- An gano wata makaranta da dalibai suke daukar darasi a ajin bukka
- Bayan haka kuma ofishin shugaban makarantar yana karkashin gindin bishiya
- Mambobin wata kungiya ne suka wallafa hotunan wannan makaranta domin mutane suga halin da makarantar ke ciki
Wata makarantar firamare a jihar Cross River ta zamo abar kwatance a wajen wata kungiya, bayan an gano cewa daliban makarantar suna daukar karatu a ajin bukka.
Lydia Yegraowo Okache da Godwin Onah suna daga cikin 'yan wannan kungiyar, kuma sune suka sanya hoton wannan makaranta bayan sunje sun kai musu gudummawar litattafan karatu.
Makarantar mai suna 'Community Primary School' dake kauyen Akpanda Itega-Egbudu dake karamar hukumar Yala cikin jihar ta Cross River, ita ce makarantar da ofishin shugaban makarantar yake a karkashin bishiya, sannan daliban ana koya musu darasi a ajin bukka.
Lydia dai ta wallafa hotunan ne domin mutane su ga halin da wannan makarantar take ciki, sannan kuma su fito da wata hanya da za su gyara makarantar ta dawo daidai.
KU KARANTA: Ni ba shegiya ba ce da ubana, martanin Umma Shehu ga Adam Zango kenan bayan wani sabon rikici ya barke tsakanin su
Ga dai hotunan makarantar a kasa:
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng