Kotu Ta Tabbatar Da Kefas Matsayin Dan Takaran Gwamnan PDP na Taraba

Kotu Ta Tabbatar Da Kefas Matsayin Dan Takaran Gwamnan PDP na Taraba

  • Kotu ta tabbatar da dan takarar kujerar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Taraba, Agbu Kefas
  • Lauyoyin Nyameh sun bayyana cewa zasu daukaka kara daga yanzu har kotun Allah ya isa
  • Dan takaran APC kuwa bai yi sa'a ba yayinda kotu tayi watsi da zabensa kuma tace ayi sabon lale

Taraba - Babbar kotun tarayya dake Jalingo, jihar Taraba, ta tabbatar da Agbu Kefas a matsayin dan takaran gwamnan jihar Taraba na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023, rahoton ThisDay.

Wannan ya biyo bayan karan da Jerome Nyameh ya shigar kotu inda ya bukaci a cire Kefas.

Nyameh, wanda ya sha kasa a zaben fidda gwanin ya cewa kotu ta soke zaben Agbu Kefas saboda bai cancanci takara a zaben ba saboda bai sayi Fom ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Bwacha

Hakazalika wani dan takaran shima, Hilkiah Buba Joda Mafindi, ya jaddada maganar cewa lallai Kefas bai sayi Fam ba.

Alkali Simon Amobeda ya yanke cewa hujjojin da aka gabatar gabansa basu gamsar ba.

Alkali saboda haka yayi watsi da karar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

J PDP
Kotu Ta Tabbatar Da Kefas Matsayin Dan Takaran Gwamnan PDP na Taraba
Asali: Getty Images

Lauyan PDP, Musa Tende, ya bayyana farin cikinsa bisa hukuncin kotun kuma yayi kira da wadanda suka shigar da kara su hada kai da Kefas wajen tabbatar da nasarar PDP a zaben.

Lauyan Nyameh kuwa, Pius D. Pius ya bayyanawa manema labarai zasu daukaka kara.

A cewarsa:

"Yanzu muka fara wannan rikici. Akwai saura kotuna biyu, saboda haka zamu daukaka kara.'

Jam'iyyar APC Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Bwacha

A wani labarin kuwa, kotun tarayya dake zamanta a Jalingo, jihar Taraba ta soke zaben Emmanuel Bwacha a matsayin dan takaran gwamnan jihar na jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wata cuta ta kama kama Nnamdi Kanu a hannun DSS, inji lauyansa

Soke zaben Bwacha ya biyo karar da daya daga cikin yan takara, David Sabo Kente, ya shigar.

Kotun ta bayyana cewa bisa hujjojin da aka gabatar gabanta, ba'ayi zaben fidda gwani a Taraba ba, rahoton ChannelsTV.

Alkali mai shari'a, Simon Amodeba, ya bada umurnin yin sabon zabe cikin kwanaki 14.

Asali: Legit.ng

Online view pixel