Bayan Karewar Wa'adi, Wani Sanata Ya Fallasa Matakin da Suke Kan Shirin Tsige Shugaba Buhari

Bayan Karewar Wa'adi, Wani Sanata Ya Fallasa Matakin da Suke Kan Shirin Tsige Shugaba Buhari

  • Sanata Orji Uzor Kalu ya magantu a kan batun tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin da majalisar dattawa ta dawo zama a yau Talata
  • Shugaban masu tsawatarwa a majalisar ya bayyana cewa a yanzu babu sanatan da ke ra'ayin tsige shugaban kasar domin matsalar rashin tsaro ta inganta
  • Tuni dai wa'adin makonni shida da majalisar ta dibawa shugaban kasar don ya magance matsalar tsaro ko a tsige shi daga kujerarsa ta cika

Abuja - Shugaban masu tsawatarwa a Majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa yan majalisar dokokin tarayya sun dawo daga rakiyar neman a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kalu ya jadadda cewa matsalar rashin tsaro wacce ita ce ta asassa kira ga tsige Shugaban kasar ta inganta sosai, Leadership ta rahoto.

Orji Kalu
Bayan Karewar Wa'adi, Wani Sanata Ya Fallasa Matakin da Suke Kan Shirin Tsige Shugaba Buhari Hoto: Vanguard
Asali: UGC

A tuna cewa wasu sanatoci a fadin jam’iyya mai mulki da mai adawa sun ba Shugaba Buhari wa’adin makonni shida ya magance matsalar rashin tsaro ko a tsige shi daga kan kujerarsa.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa A 2023: Tinubu Na Da Karfin Da Zai Iya Farfado Da Najeriya, Yahaya Bello

Majalisar dattawan ta tafi hutunta na shekara jim kadan bayan bayar da wa’adin kuma tuni wa’adin ya cika.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Leadership ta rahoto cewa yayin da majalisar dattawan ta dawo a ranar Talata, ana ta sa ran yan majalisar za su waiwayi barazanar tsigewar da aka yiwa Buhari.

Amma Sanata Kalu, wanda ya kore fargabar cewa majalisar na iya tsige Buhari daga dawowa, ya ce babu dan majalisar da zai samar da adadin sa hannun da ake bukata don tsige imma Shugaba Buhari ko shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.

Kalu ya kara da cewa koda an sake gabatar da irin wannan batu a zauren majalisar dattawan, zata mutu murus da kanta.

Kalu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Litinin da dawowar majalisar dattawa bayan hutun watanni biyu.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Wa'adi ya cika, majalisa ta fadi ranar da za ta sake duba batun tsige Buhari

Ya ce:

“Batun tsigewar lamari ne da babu ita. Babu wanda ke magana a kanta. Koda sun yi kokarin yi, ba za su yi nasara ba saboda muna da yawan hana hakan.
“Babu laifi dan dan majalisa ya zo da barazanar tsigewa amma shin za su yi nasara? A’a! Don haka, a iya sanina, babu wani tattaunawa game da tsige Buhari saboda tsaro ya inganta.
“Muna ta haduwa da shugabannin tsaro kuma wasu daga cikinsu sun kasance a wajen kuma za su iya tabbatar da cewa lamarin tsaro ya inganta kuma zai ci gaba da inganta.”

Bayan Cikar Wa’adi, Majalisar Dattawa Za Ta Sake Duba Batun Tsige Buhari Ranar Talata

A baya mun ji cewa wa'adin makwanni shida da aka dibarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya warware matsalolin tsaron Najeriya sun shude, har yanzu abubuwa basu kankama ba.

A cewar rahoton jaridar The Guardian, majalisar dokokin Najeriya za ta sake zama a ranar Talata mai zuwa, 20 ga watan Satumba don sake duba batun tsige shugaban.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Kame Tukur Mamu ba zai hana mu ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja ba

Idan baku manta ba, rahotanni sun karade Najeriya a ranar 27 ga watan Yuli cewa, majalisar dattawa ta dago batun tsige Buhari saboda ta'azzarar lamurran tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng