An Gano Miliyoyin Kuɗin da 'Yan Fashi Suka Sace a Motar Dakko Kudi a Gidan Tsohon DSS
- Yan sanda sun damke tsohon jami'in DSS da wasu mutum Tara kan zargin fashin Motar dakon kuɗi a jihar Abiya
- Kwamishinar 'yan sandan jihar, Misis Jenet Agbede, tace sun samu sama da miliyan 10 daga cikin kudaɗen da aka sace
- Jami'am tsaro sun kuma kwato makamai masu hatsari daga hannun tawagar yan fashin da ake zargi
Tsohon jami'in hukumar DSS, Prosper Israel, da wasu mutum tara sun shiga hannu kan zargin hannu a fashin miliyoyin naira daga wata Mota mai dakon kudi tare da kashe mai rakiya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Da take nuna waɗanda ake zargi a Hedkwatar hukumar 'yan sanda dake Umuahia, babban birnin Abiya, jiya Litinin, kwamishinar yan sanda, Misis Jenet Agbede, tace an samu N10,184,000 a hannunsu.
A rahoton Leadership, Ta ƙara da cewa waɗanda suka shiga hannun na daga cikin tawagar mutum 14 da suka mamayi Motar a babban titin Enugu zuwa Patakwal, kusa da Ntigha Junction a ƙaramar hukumar Isiala Ngwa ta arewa.
Sauran mutum Tara sun haɗa da, Adesoji Adeniyi ‘Soji’ (jihar Ondo), Nnamdi Nwaosu, ‘Prophet’ (jihar Ribas), Nwachukwu Albert, ‘White’, Mai sulƙen farko (Delta) da Chinwendu Israel (Abia).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sauran waɗanda ake zargin sune; Felix Ajalaja (Ondo), Moshood Opeyemi (Osun), Matthew Christmas Aluwa (Delta), Azubuike Amaefula ‘Zubby’ (Abia) da kuma Monday Samuel, (jihar Delta).
Kwamishinae yan sandan tace:
"Waɗanda ake zargin ɗaya bayan ɗaya ba tare da tilasta musu ba suka amsa cewa suna cikin ƙungiyar fashi da makami ta mutum 14 da suka maida hankali wajen kai wa motar kudi hari."
"Kuma sun ce kusan watanni biyu kafin wannan hari da dubunsu ta cika, motar kuɗin na kan idonsu."
An gano makamai a hannun mutanen
Bugu da ƙari, shugabar yan sandan jihar Abiya tace sauran kayan aikin da aka kwato a hannun su sun haɗa da Bindigar Machine Gun cike da alburusai 53, AK-47 guda 13 da Alburusai 1,749.
A wani labarin kuma 'Yan sanda sun Kama Wani Kasurgumin Ɗan Bindiga da Sojan Bogi a Jihar Zamfara
Yan sanda sun ce sun kama wani babban ɗan bindiga da ya addabi mutane, Umar Namaro, a jihar Zamfara .
Muhammed Shehu, kakakin yan sandan jihar yace dakaru sun kama wani Sojan Bogi ɗauke da muggan makamai a jihar.
Asali: Legit.ng