Kai tsaye: Yadda jana'izar Sarauniya Elizabeth II ke Gudana Burtaniya

Kai tsaye: Yadda jana'izar Sarauniya Elizabeth II ke Gudana Burtaniya

Da karshe, a yau Litinin ne kasar Burtaniya ta fara bikin karshe na binne sarauniya Elizabeth da ta rasu a makon da ya gabata.

Bayan sharbar kukan jimami da kuma bankwana da sarauniyar, shugabannin duniya sun taru a yau 19 ga watan Satumba domin bison Elizabeth II.

Ku biyo mu domin kawo muku yadda ake jana'izar kai tsaye daga Burtaniya.

Westminster Abbey, nan ne wurin da aka daura auren sarauniya Elizabeth da yarima Phillip a shekarar 1947.

Legit.ng ta samo cewa, anan ne aka nada ta sarautar Ingila a 1953, kuma an yi bukukuwa daban-daban na saraunta a wurin.

An sanya gawar sarauniyar Ingila cikin taskar adana gawa, a inda aka ajiye mijinta da ya rasu bara

Rahoton da muke samu ya bayyana, cewa, an riga an snaya sarauniya Elizabeth II cikin ma'ajiyar gawa da aka tanada tuntuni don irin wannan ranar.

Wata makala da masarautar Ingila ta wallafa ta ce, za ta hade ne da mijinta da ya rasu bara, Duke na Edinburgh, Yarima Phillip.

Bayan yiwa sarauniya addu'a da sa albarka daga bakin shugaban fastocin Ingila, za a binne ta Winsor Castle.

Gawar Sarauniya Elizabeth II ta isa cocin St. George

Yanzu muke samun labarin cewa, gawar sarauniyar Ingila ya iso cocin St. George a Windsor Castle don yin addu'o'i kafin daga karshe a saka ta a kabarinta

Dubban mutane ne suka taru a Landan domin sallama da sarauniya, sai dai mutum 800 ne aka amince halarci hidimar cocin na St George.

Wadanda za su halarci hidimar galibi shugabannin duniya ne, 'yan gidan sarauntar da dai sauran jiga-jigan mutane.

Kalli bidiyon lokacin da aka kawo ta:

An bar shugaban Amurka Biden ya shiga wurin jana'iza da tawagarsa motocinsa, sauran shugabanni na cikin motoci bas

Bidiyo ya nuna lokacin da aka bar shugaban kasar Amurka Joe Biden ke shiga wurin jana'aizar sarauniyar Ingila Elizabeth da tawagar motocinsa.

Sai dai, sauran shugabanni sun zo ne a cikin motocin bas da aka dauko su tare.

Kalli bidiyon:

Shugabannin duniya sun halarci taron jana'izar

Bidiyo ya nuna lokacin da shugaban kasar Kenya, William Ruto ya dura Burtaniya domin halartar jana'iza.

Hakazalika, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo na Najeriya ya halarci taron.

Kalli bidiyo:

An wallafa waken yabo ga sarauniya Elizabeth II

A shafin Twitter na gidan Sarautar Ingila, an yada bidiyo da dama na yadda ake gudanar da gangamin jana'izar a yau Litinin 19 ga watan Satumba.

Tuni dai aka wallafa wani wake da Laureate Simon Armitage ta rubuta don girmama sarauniya.

Ga dai kadan daga bidiyon da aka yada:

Online view pixel