Gwamnatin Katsina Ta Ware N1.5bn Domin Kawo Karshen Matsalar Rashin Tsaro

Gwamnatin Katsina Ta Ware N1.5bn Domin Kawo Karshen Matsalar Rashin Tsaro

  • Gwamnatin Aminu Bello Masari na jihar Katsina ta ware zunzurutun kudi har naira biliyan 1.5 domin kawo karshen matsalar rashin tsaro
  • Masari ya sha alwashin baiwa hukumomin tsaro cikakken goyon baya domin yin maganin miyagu a jihar
  • A ranar Asabar ne aka yaye yan sa-kai 600 da za su taimakawa jami'an tsaro wajen fatattakar miyagu a lungu da sako na jihar

Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta ware kudi naira biliyan 1.5 domin yakar rashin tsaro a jihar.

Gwamnan jihar, Aminu Masari, ne ya bayyana hakan yayin bikin yaye yan sa-kai 600 a kwalejin hukumar tsaro ta NSCDC a ranar Asabar, Daily Trust ta rahoto.

Masari, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Muntari Lawal, ya jinjinawa yan sa-kai wadanda suka dauki alkawarin zuwa kowani lungu da sako na jihar don taimakawa jami’an tsaro a yaki da fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran laifuka.

Bello Masari
Gwamnatin Katsina Ta Ware N1.5bn Domin Kawo Karshen Matsalar Rashin Tsaro Hoto: The Sun
Asali: Facebook

Gwamnan ya jadadda jajircewar gwamnatinsa na taimakawa hukumomin tsaro da mutanen da suka sadaukar da kansu don taimakawa jihar a yaki da rashin tsaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

“Gwamnatina ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na taimakawa hukumomin tsaro, kungiyoyi da kuma mutane masu mutunci a yaki da rashin tsaro a jihar.”

A nashi jawabin, mai ba gwamnan shawara kan tsaro, Alhaji Ibrahim Katsina, ya ce yan sa-kai 600 sun kasance maza da mata masu matukar mutunci da kwalayen karatu da suka hada da NCE, Difloma, Digiri, Digir-gir da kuma digirin digir-gir, rahoton Premium Times.

A jawabinsa, kwamandan kwalejin NSCDC, Babangida Abdullahi, ya ce an horar da mutane kimanin makonni biyu a kwalejin kan makamai da sauran dabaru na yadda za a magance rashin tsaro.

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1, Sun Sace Manoma 3 A Kaduna

A wani labarin kuma, mun ji cewa yan bindiga sun yi garkuwa da manoma uku yayin da suka kashe wani mutum daya a garin Kurgin Gabas da ke yammacin karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

Kungiyar ci gaban masarautar Birnin wato BEPU ta ce tun a ranar 1 ga watan Satumba yan bindiga suka toshe babban titin Birnin-Gwari-Funtua sannan suka kwace motoci fiye da 30 ciki harda manyan motocin daukar kaya, The Nation ta rahoto.

Kungiyar BEPU a cikin wata sanarwa da shugabanta, Ishaq Usman Kasai ya saki, ta kuma bayyana cewa matafiya da dama da aka sace a ranar 1 ga watan Satumba har yanzu ba a sako su ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel