Gwamna Soludo ya Wanke Fulani, Ya Bayyana Wadanda ke Assasa Rashin Tsaro a Anambra

Gwamna Soludo ya Wanke Fulani, Ya Bayyana Wadanda ke Assasa Rashin Tsaro a Anambra

  • Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya fallasa wadanda ke assasa rashin tsaro da yayi kamari a jiharsa
  • Soludo ya bayyana cewa, kashi 100 na wadanda aka kama sun garkuwa da mutane da kisa duk 'yan kabilar Igbo ne
  • Yace babu wani a ce ba a san masu laifukan yankunan kudu maso gabas ba, ana kama su kuma duk matasn Igbo ake kamawa

Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya yi bayanin dalilin da yasa rashin tsaro da garkuwa da mutane suka yi kamari a jihar, inda yace halin da tattalin arzikin jihar ke ciki yasa 'yan ta'adda suka makale.

Yace a yayin da rashin tsaro yayi kamari a jihar, mulkinsa ya yi duk abinda ya dace wurin ganin karshen matsalar.

Charles Soludo
Gwamna Soludo ya Wanke Fulani, Ya Bayyana Wadanda ke Assasa Rashin Tsaro a Anambra. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Soludo wanda ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin zantawa da shirin Siyasa a Yau na gidan talabijin din Channels, yace wadanda ke ta'addanci a jihar duk 'yan kabilar Igbo ne.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: An kai makura, dalibai sun toshe hanyar filin jirgin sama suna zanga-zanga

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriyan ya kara da cewa, akasin yadda ake ta bayyanawa na cewa ba a san wadanda ke ta'addanci ba, an san su.

"'Yan ta'adda ne. Wasu daga cikin masu laifin suna boyewa a karkashin neman kafa kasar Biafra amma IPOB sun nisanta kansu daga wadannan masu laifukan.
“Masu garkuwa da mutane ne kuma masu aikata laifuka ne saboda suna cin kasuwarsu shiyasa suke yi. Babu shakka Anambra jiha ce mai arziki a kudu maso gabas, don haka wannan jihar ce suka fi samun kudin fansa kuma don haka suka fi zama nan.
"Idan kai 'dan acaba ne dake shiga daji, ka koyi harbi kuma ka shiga kungiyar ta'addanci bayan hakan kuke sace mutane kuna samun kudi. Wannan ba zai bar irin wadannan su koma acaba ba.
“Ba 'yan bindiga ne ba da ba a sani ba, an san su ta yadda ba a iya kama su a take. Amma ina fada muku ana kama su da yawansu kuma sun san cewa Anambra ba mafakarsu bace."

Kara karanta wannan

Dukkan Yan Bindigan Da Aka Kama A Anambra Yan Kabilar Ibo Ne, In Ji Gwamna Soludo

Soludo ya kara da cewa:

"Bari in fada muku gaskiya, kashi 100 na wadanda aka kama 'yan kabilar Igbo ne, babu wani batun cewa wasu daga wani wuri ne ke shigowa, dukkansu Igbo ne.
“Anambra na samun shigowar 'yan kabilar Igbo daga jihohin Kudu maso gabas da sauran sassan Najeriya. A farko dai mutanen da aka kama Igbo ne daga jihohin kudu maso gabas ba daga Anambra ba.
"Amma da aka cigaba, mun gano cewa da yawan matasa suna shiga harkar kuma ba mu sassauta musu, muna yin abinda ya dace."

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1, Sun Sace Manoma 3 A Kaduna

A wani labari na daban, rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun yi garkuwa da manoma uku yayin da suka kashe wani mutum daya a garin Kurgin Gabas da ke yammacin karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

Kungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari wato BEPU ta ce tun a ranar 1 ga watan Satumba yan bindiga suka toshe babban titin Birnin-Gwari-Funtua sannan suka kwace motoci fiye da 30 ciki harda manyan motocin daukar kaya, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mabaraci Ya Tsallake Rijiya Da Baya Yayinda Aka Kamashi Kudi N500,000 a jihar Legas

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng