An Haramta Amfani Da 'Mini Skirt' A Matsayin Unifom A Makarantun Wata Jihar Kudancin Najeriya

An Haramta Amfani Da 'Mini Skirt' A Matsayin Unifom A Makarantun Wata Jihar Kudancin Najeriya

  • Gwamnatin Jihar Anambra ta hana yan makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar saka gajerun siket a matsayin unifom yayin zuwa makaranta
  • Farfesa Ngozi Chuma-Udeh, kwamishinan ilimi na jihar Anambra ne ta bada sanarwar tana mai cewa dabi'ar ba tarbiya bane mai kyau dole kuma a dakatar da hakan
  • Chuma-Udeh ta ce an umurci sakatarorin ilimi na jihar su tabbatar dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu su tabbatar sun bi dokar

Jihar Anambra - Gwamnatin Jihar Anambra ta haramta saka gajerun siket wato 'mini skirt' a matsayin unifom a dukkan makarantun jihar, Premium Times ta rahoto.

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Farfesa Ngozi Chuma-Udeh, ne ta bayyana hakan a Awka a ranar Lahadi tana mai cewa sanarwar haramcin ya zama dole domin makarantu za su dawo hutu a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Fasto da mabiyansa sun sha bulala yayin da wasu tsageru suka farmaki coci a jihar Arewa

Daliban Makaranta
An Haramta Amfani Da 'Mini Skirt' A Matsayin Unifom A Makarantun Wata Jihar Kudancin Najeriya. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

Ta ce tuni an sanar da sakatarorin ilimi na makarantun gwamnati da masu zaman kansu game da dokar haramcin.

Rashin tarbiya ne saka mini skirt - Farfesa Chuma-Udeh

Kwamishinan ta yi tir da sabon yayin da ake yi na saka mini siket a matsayin kayan makaanta kuma ta ce rashin tarbiya ne kuma ba za a amince yan makaranta su rika yin hakan ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta ce:

"A matsayin dalibai ya kamata ka yi shiga tsaf-tsaf, ta nuna halaya masu kyau ba shiga irin ta rashin tarbiya ba yayin zuwa makaranta.
"Ta ce abin da aka amince shine tsawon unifom ya rufe gwiwa ba ya gaza kai wa gwiwa ba, wanda shine sabon yayin da ke bazuwa a makarantu."

Kwamishinan Ilimin ta ce an bukaci sakatarorin ilimi su tabbatar da dukkan makarantun jihar sun bi umurnin don kyautata rayuwar daliban a gaba.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamna Ganduje Ya Ware biliyan N1.2 Don Ayyukan Hanyoyi 42

Chuma-Udeh ta bukaci sakataroron su bawa daliban tarbiyya da ta dace saboda su zama masu halaye na gari su zama manya masu amfani idan sun girma.

Hotuna: Kakakin Majalisar Najeriya, Gbajabiamila Ya Koma Makaranta A Amurka

A wani rahoton, kakakin Majalisar Wakilai ta Najeriya, Femi Gbajabiamila, a halin yanzu yana karatun wani kwas a Makarantar Ilimin Koyon Aikin Gwamnati ta John F Kennedy da ke Jami'ar Kasuwanci ta Harvard.

Mr Gbajabiamila, wanda lauya ne, ya wallafa hotunansa a cikin aji tare da wasu daliban yan kasashen waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164