Wani Babban Basarake a Oyo, Abdul-Rasheed Shehu, Ya Rasu

Wani Babban Basarake a Oyo, Abdul-Rasheed Shehu, Ya Rasu

  • Ɗaya daga cikin Sarakunan dake da alhakin naɗa Sarkin Oyo, Alh Abdul-Rasheed Shehu, ya riga mu gidan gaskiya da safiyar nan
  • A wata sanarwa da gwamnatin ƙaramar hukumar Oyo ta gabas ta fitar tace za'a masa Jana'iza da misalin ƙarfe 4:00 na yamma
  • Marigayi Alapinni na Oyoland ya rasu ne yayin da ake cigaba da tantance masu neman kujerar Alaafin Of Oyo

Oyo - Ɗaya daga cikin sarakunan da ake kira 'Oyomesi', Alapinni na ƙasar Oyo, High Chief Abdul-Rasheed Shehu, ya riga mu gidan gaskiya da safiyar nan ta Lahadi.

Wata majiya daga cikin iyalan gidan Sarautar da suka samu masaniya, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa Sarkin ya rasu ne da safiyar nan bayan fama da wata rashin lafiya da ba'a bayyana ba.

Kara karanta wannan

Sojojin Sama Sun Yi Luguden Wuta A Sansanin Gogarman Yan Bindiga Bello Turji

High Chief Abdul-Rasheed Shehu.
Wani Babban Basarake a Oyo, Abdul-Rasheed Shehu, Ya Rasu Hoto: Vanguardngr.com
Asali: UGC

Yace za'a masa Jana'iza anjima da yammaci kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada a harabar gidansa.

Idan baku manta ba ɗaya daga cikin 'ya'yan Marigayin mai suna Badira, ta auri Marigayi Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi na III.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnati ta tabbatar da rasuwar

The Nation tace Gwamnatin ƙaramar hukumar Oyo ta gabas ta tabbatar da rasuwar Basaraken. A sanarwan da ta fitar tace, "Innalillahi wa'inna Ilaihii Raji'uun."

"Cikin raunanannar zuciya da miƙa lamari ga Allah, shugabancin ƙaramar hukumar Oyo ta gabas na bakin cikin sanar da rasuwar Alapinni na Oyoland, Alh Abdul-Rasheed Shehu, da safiyar Lahadin nan 18 ga watan Satumba."
"Za'a masa jana'iza da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin yau a gidansa, Allah ya jikansa ya sa Aljanna ta zame masa makoma."

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Mamacin bai samu halartar taron tantance masu neman kujerar Sarautar Alaafin Of Oyo ba, wanda har yanzun ba'a kammala ba.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Fasa Auren Budurwa Saboda Ta Ki Bayyana Wanda Ya Bata Kyautan IPhone13 ProMax

A wani labarin na daban kuma Gini Bene Mai Hawa 4 Ya Rufto Kan Mutane, Ana Fargaban Ya Rutsa Da Gommai

Wani ginin bene mai hawa hudu a titin Imam Street Uyo, babbar birnin jihar Akwa Ibo ya rufta da mutanen da ba'a san adadinsu ba har yanzu.

An tattaro cewa wannan gini ya rufto kan wani ginin daban misalin karfe 6:30 na yammacin Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: