Jerin Sunayen Yan Siyasar Najeriya Da Suka Mallaki Fitattun Jaridu Da Tashoshin Talbijin
A Najeriya da sassa da dama na duniya, siyasa da aikin jarida na tafiya ne kafada da kafada, inda mutane daga wadannan bangarori ke gwabzawa yayin da wasu ke cin moriyar dukkanin bangarorin biyu a lokaci daya.
Wasu manyan yan siyasar Najeriya sun mallaki wasu manyan kafofin watsa labarai, inda a wasu gabar yake kasancewa rade-radi.
Sai dai kuma a wannan shafin, Legit.ng ta binciko zahirin gaskiya inda ta tattaro jerin wasu manyan yan siyasa a kasar wadanda suka zuba jari sannan suke kama kudi a bangaren jarida.
Ga jerin sunayen yan siyasar Najeriya da gidajen jaridun da suka mallaka:
- Tsohon Gwamna James Onanefe Ibori - Daily Independent (1997)
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu – Jaridar The Nation, TVC, Radio Continental, Adaba FM
- Sanata Ben Murray Bruce - Rhythm FM, Silverbird TV (1980)
- Tsohon Sanata Chris Anyanwu - Hot FM
- Tsohon dan takarar shugaban kasa na APC Sam Nda-Isaiah Jaridar Leadership
- Tsohon dan takarar gwamna na PDP, Jimoh Ibrahim - National Mirror
- Tsohon dan takarar gwamna, Ifeanyi Ubah - Authority Newspaper
- Jigon PDP, Raymond Dokpesi - AIT, Ray Power FM
- Tsohon Gwamna Orji Uzor Kalu - Daily Sun (2001)
- Atiku Abubakar - Atiku TV
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnan Arewa Ya Mance Da Batun Tinubu, Ya Fadi Wanda Zai Sa Ya Gaji Buhari Da Yana Da Iko
A wani labarin, gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa da ace yana da ikon zartar da hukunci da babu makawa takwaransa na jihar Ekiti, Kayode Fayemi zai nada a matsayin shugaban kasa.
Sani Bello ya bayyana Fayemi wanda ya nemi tikitin takarar shugaban kasa na APC, a matsayin aminin jiharsa tunma kafin ya zo neman kuri’u a kudirinsa na son zama shugaban kasa.
Gwamnan na Neja ya bayyana hakan ne yayin da ya tarbi Fayemi a gidan gwamnati da ke garin Minna, babbar birnin jihar a yammacin ranar Lahadi, Leadership ta rahoto.
Asali: Legit.ng