Yadda Asibiti Suka Rike Gawar Yarinya Saboda Iyayenta Sun Kasa Biyan N400,000 na Magani
- Asibitin Koyarwa na Jami'ar Benin sun rike gawar yarinya mai shekaru 12 saboda iyayenta sun gaza biyan N400,000 na maganinta
- Kamar yadda mahaifin yarinyar ya sanar, ya roki asibitin amma sun kammala gawarta a wurinsu har sai sun biya bashin
- Ya sanar da cewa basi da hanyar samun wadanda kudaden saboda ciwon da yarinyar tayi ya wawushe musu 'dan kudin da suka samu
Edo - Asibitin koyarwa na jami'ar Benin, UBTH sun rike gawar matashiyar yarinya mai shekaru 12 mai suna Glory Ekeleyede saboda iyayenta sun kasa biyan kudin asibitinta.
Ekeleyede kamar yadda Kamfanin Dillancin Najeriya ya tattaro ta mutu a asibitin a ranar 15 ga watan Yuli yayin wata jinya da tayi.
Kamfanin Dillancin Labari ya tattaro cewa, dukkan kudin da ta sha magani zuwa na kwanciya asibitin ya kai N400,000.
Wata majiya tace rashin biyan kudin ne yasa asibitin suka rike gawar matashiyar yarinyar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mahaifin yarinyar mai suna Samson Ekeleyede mai shekaru 66 ya koka kan cewa ciwon diyarsa ya jefa shi cikin matsalar rashin kudi.
Yace iyalan sun dinga aron kudi domin biya kudin asibiti tare da wasu bukatu, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Manomin wanda matarsa 'yar kasuwa ce, yace iyalansa ba su cin abinci a kowacce rana saboda dukkan kudinsu ya kare kan diyarsu da ta rasu.
“Na koyi dinki amma ba wannan sana'ar nake yi ba. Ina yin kananan ayyuka ne domin ciyar da yarana. Matata tana siyar da kayan miya a kasuwa kuma da hakan muke maneji."
- Yace.
A bangaren kokarin da ya dinga kafin mutuwar yarinya, Ekeleyede yace:
"Yarinyar ta mutu a ranar 15 ga watan Yuli kuma tun daga lokacin take ma'adanar gawawwaki.
“Na je na roke su amma sun ce ba yin kansu bane. Sun ce sai na biya, a cewarsu sun yi mata amfani da oxygen shiyasa kudin yayi yawa. Kun yi amfani da Oxygen din bai yi amfani ba.
"Idan da yarinyar tana nan da ranta, wani abu ne daban. Amma sun ce sai na biya, ba zasu saki gawarta ba balle mu birne. Na dade ina zuwa amma sun ki.
“Na sanar da daya daga cikin fastocin cocinmu, abun ya taba shi kuma ya rubuta wasika zuwa gwamnati. Yace in kai ofishin mataimakin gwamna.
“A lokacin gwamnan ya je hutu, mukaddashi ne. A ranar da na kai ita ce ranar da Gwamna Obaseki ya dawo, na bai wa PRO din shi.
“Wannan ne faston cocinmu yace in bai wa. Ina tunanin ya kara da kiran sunan matar mataimakin gwamnan. Tun bayan nan muna ta jira amma babu abinda ya faru."
A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun UBTH, Uwaila Joshua, tace:
"An san cewa idan har ka kwanta aka kula da kai dole ka biya kudi."
Asali: Legit.ng