Yan Ta'adda Sun Karbi N19m, Da Kwale-Kwale A Matsayin 'Harajin Tsaro' Daga Mutanen Wasu Garuruwa A Zamfara

Yan Ta'adda Sun Karbi N19m, Da Kwale-Kwale A Matsayin 'Harajin Tsaro' Daga Mutanen Wasu Garuruwa A Zamfara

  • Yan bindiga suna cigaba da cin karensu babu babbaka a wasu yankuna na Jihar Zamfara da sauran jihohin arewa maso yamma da tsakiya
  • Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addan sun karbi makuden kudi har Naira miliyan 19 har da kwale-kwale daga mutanen wasu kauyuka a Anka, Jihar Zamfara
  • Wani shugaban al'umma a Anka ya tabbatar da lamarin yana mai cewa ba sabon abu bane domin dan mutanen ba su biya ba, za su zauna lafiya ba

Zamfara - Kimanin garuruwa 14 a Jihar Zamfara sun yi karo-karo sun bawa yan ta'addan da ke Anka da Bukkuyum Naira miliyan 19 da kwale-kwale a harajin basu kariya.

Wani mai wallafa labarai, Yusuf Anka, wanda shima dan garin ne ya shaidawa Premium Times cewa garuruwa da dama a Anka suna tara kudin kariyar su biya yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da mazauna suka tsere, an hallaka dan banga, an sace mutane a Neja

Kwale-Kwale
Yan Ta'adda Sun Karbi N19m, Da Kwale-Kwale A Matsayin 'Harajin Kariya' Daga Wasu Garuruwan Zamfara. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce yan ta'addan sun kakabawa garuruwan harajin daf da za a shigo damina.

Mr Anka ya ce mazauna garuruwan ba su da wani zabi illa tara wannan kudin domin gudun kada yan ta'addan su kawo musu hari yayin aiki a gonakinsu ko ma a gidajensu.

An wanda ya wallafa bidiyon bincike kan ta'addanci a baya-bayan nan mai taken 'The Bandits Warlords of Zamfara' ya ce:

"Dukkan garuruwan na karkashin Anka ne kuma an umurci su tara kudi don kariya. Wasu garuruwan sun biya kudinsu watanni biyu da suka gabata. Amma jimilar kudin ya kai Naira miliyan 19."

Ya ce mutanen garin Yar Sabaya ne suka siya kwale-kwalen. Rafi guda biyu ne suka zagaye garin Anka sannan akwai wasu kananan rafin a kewaye da shi.

Mr Anka ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ku Zabi Wadanda Suka Fara Yi Muku Aiki Suka Gaza, El-Rufai Ya Fadi Dalili

"Yan bindigan sun umurci garuruwa daban-daban su tara musu kudi saboda su kyalle su suyi aiki a gonakinsu ba tare da kai musu hari ba. Ba wannan ne karon farko da suke biyan harajin ba."

Adadin harajin da kauyukan na Zamfara suka biya - Yusuf Anka

Ba bada sunayen kauyukan da suka biya kudi da adadin da suka biya kamar haka:

Jargaba N1.6m, Birnin doki N1m, Tangaram N1.5m (daga baya suka kara N2.5m), Jarkuka N1.5m, Tuntuja N500,000, Tsafta N1m, Tudun magaji N2m, Kadaddaba N820,000, Tudun kudaku N950,000, Gargam N1m, Kwanar Maje N900,000, Yar tumaki N1m, Bawar Daji N1.7m, Tungar Liman N6m da Makakari N430,000.

Wani jagoran al'umma ya tabbatar da biyan harajin

Wani jagoran al'umma a Anka wanda ya nemi a boye sunansa saboda tsaro ya ce sun san da batun biyan harin da yan ta'addan suka kakabawa mutane.

Yan bindiga na kwantawa da matanmu da yayanmu mata saboda rashin biyan harajin N2m – Mazauna Zamfara

Kara karanta wannan

'Yan Ta'addan Boko Haram Kasurguman 'Yan Damfara ne, Shugaba Buhari

A wani rahoton, mazauna garuruwa biyar da ke karkashin yankin Kurya Madaro a karamar hukumar Kaura Namoda da ke jihar Zamfara sun tsere daga gidajensu bayan yan bindiga sun koma yiwa matansu da yayansu mata fyade saboda rashin biyan kudin harajin da suka daura masu.

An tattaro cewa mazauna garuruwan da abun ya shafa sun zabi tserewa don tsira daga ci gaban hare-hare bayan sun gaza biyan yan bindiga naira miliyan 2 da suka daurawa kowannensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164