Luguden Sojojin Najeriya Ya Halaka Hatsabibin Dan Ta'adda, Amir Bashir, a Borno

Luguden Sojojin Najeriya Ya Halaka Hatsabibin Dan Ta'adda, Amir Bashir, a Borno

  • Jirgin yaƙin rundunar sojin Najeriya ya samu gagarumar nasara a wani samame da aka kai mafakar mayaƙan ISWAP a Borno
  • Zakazola Makama, yace luguden wutan jirgin ya yi ajalin ƙusoshin kungiyar guda uku da tarin mayaƙa
  • Jirgin ya kai farmaki ne kan sansanonin yan ta'adda uku duk a yankin ƙaramar hukumar Kukawa dake Borno

Borno - Kwamandojin ƙungiyar 'yan ta'adda (ISWAP) guda uku sun sheƙa barzahu sakamakon luguden wuta jirgin yaƙin sojin Najeriya a jihar Borno.

The Cable ta ruwaito cewa Amir Bashir, wanda aka fi sani da 'Iblis' watau Sheɗan na ɗaya daga cikin kwamandojin da Sojojin suka aika ƙabari a samamen.

Jirgin yaƙi a sama.
Luguden Sojojin Najeriya Ya Halaka Hatsabibin Dan Ta'adda, Amir Bashir, a Borno Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A cewar Zagazola Makama, mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, Bashir ga kasance lamba ɗaya a fagen harbi na kungiyar ISWAP, wanda ke nufin abin hari daga ɓoye.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Ruwa Ta Tashi Al'ummar Garuruwa Sama da 10 a Jigawa, Ta Cinye Rayukan Mutane

Muhammad Balge, shugaban fannin shari'a da kuma mataimakinsa na farko, Mallam Chiroma, sune sauran kwamandojin 'yan ta'ddan biyu ruwan bama-bama ya aika inda ba'a dawowa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayanai sun nuna cewa dakarun sama na rundunar Operation Haɗin Kai ne suka kaddamar da harin, wanda aka kai ranar Laraba kan sansanonin yan ta'adda da ke Rino, Jibularam da Kangarwa, ƙaramar hukumar Kukawa, jihar Borno.

An ruwaito Zagazola Makama na cewa, "Ruwan wutan farko da aka nufi mafakar yan ta'adda da wurin ɗaukar horonsu a Rinu, ya yi ajalin mayaƙa da yawan gaske."

"A wata fitar bayan samun sahihan bayanan sirri, dakarun Operation Haɗin Kai sun sheke yan ta'adda da dama dake tafiya cikin motoci biyu a hanyar Kangarwa dake Kukawa."
"Bayan samun bayanai, nan take jirgin yaƙin NAF ya tashi zuwa wurin, ya saki ruwan wuta, yan ta'adda da dama suka mutu. Sojojin ƙasa da aka tura yankin sun gano cewa an kashe mayaƙan da yawa."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsagin Wike Sun Bazo Wuta, Atiku Ya Kafa Sharuɗdan Tunɓuke Shugaban PDP Na Ƙasa

Binciken gaskiya kan Tukur Mamu

A wani labarin kuma Gaskiya Ta Fito Kan Ƙishin-Ƙishin Ɗin Tukur Mamu Ya Fallasa Masu Ɗaukar Nauyin 'Yan Ta'adda a Arewa

Mun gudanar da binciken gano gaskiya kan wani rubutu da ake yaɗawa a Facebook da wasu kafafen sada zumunta kan Tukur Mamu.

Rubutun dai ya yi ikirarin cewa mai shiga tsakanin yan ta'adda da FG don sako Fasinjojin jirgin Kaduna ya fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262