Sarkin Kano Ya Naɗa Sheikh Aminu Daurawa Matsayin Limamin Masallacin Jami'ar Skyline

Sarkin Kano Ya Naɗa Sheikh Aminu Daurawa Matsayin Limamin Masallacin Jami'ar Skyline

  • Bayan shekaru uku da barin Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa ya samu babban mukamin limanci
  • Mai Martaba Sarkin Kano ya nada babban Malamin matsayin Limanin Masallacin Jami'ar Skyline
  • Sarkin na Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nada mataimakan limami guda uku

Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya naɗa babban malamin addinin Musuluncin nan, Assheikh Aminu Ibrahim Daurawa, a matsayin limamin sabon masallacin jami'ar Skyline.

Jami'ar Skyline na daya daga cikin jami'o'in kudi masu zaman kansu a jihar Kano.

Yana tsohon ginin dogon bankin a kusa sakatariyar Audu Baƙo da ke Kano.

An yi bikin nadin ne a fadar mai martaban a safiyar Alhamis, 15 ga watan Satumba, 2022, rahoton TDR Hausa.

Bikin ya sami halartar manyan jami'ai na fadar Kano.

Malam Daurawa
Sarkin Kano Ya Naɗa Sheikh Aminu Daurawa Matsayin Limamin Masallacin Jami'ar Skyline Hoto: The Daily Reality Hausa
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin Yaƙin Sojoji Ya Kai Sabon Harin Bama-Bamai Maɓoyar Bello Turji a Zamfara

Sarkin ya yi addu'a ta musamman tare da yabawa Shehin Malamin game da ƙoƙarin wayar da kan mutane zuwa ga tafarkin Allah.

A cewar mai martaba:

"Muna ganin irin abubuwan da malam yake yi na wayar da kan al'umma da nusarwa. Muna yi wa Malam godiya da addu'ar fatan alheri. Muna ganin bidiyoyi na karatuttuka iri-iri, Allah Ya saka da alheri."

Sauran waɗanda mai martaba sarkin ya naɗa, a matsayin na'iban Malam Daurawa sun haɗa da Dr. Jamilu Lawan Ajiya Fagge, daga jami'ar DutsinMa, a matsayin na'ibi na ɗaya. Sai Malam Anas Muhammad Madabo, a matsayin na'ibi na biyu. Sai kuma Dr. Muhammad Sulaiman Abdullahi, daga jami'ar Bayero, a matsayin na'ibi na uku.

Sheikh Malam Aminu Daurawa ya yi wa sarki addu'ar fatan alheri da fatan zaman lafiya ga al'ummar jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel