Jerin Shugabanni 6 Da Aka Ki Gayyata Taron Jana'izar Sarauniya Elizabeth
An yi jana'izar Sarauniyar Elizabeth II ranar Litinin 19 ga watan Satumba, 2022 a birnin Landan.
Akalla shugabannin kasashe da manyan mutane fiye da 500 suka halarci jana'izar da akayi a birnin Landan.
An yi taron a babban dakin Westminster Abbey daukar mutum 2,200.
Amma akwai wasu shugabannin kasashe da ba'a aikewa takardar gayyata ba,a cewar wakilin BBC James Landale.
SkyNews ta bayyana dalilin rashin gayyatar wadannan kasashe.
Ga jerinsu:
1. Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Shugaban Kasar Belarus, Alexander Lukashenko
3. Shugaban Kasar Myanmar Min Aung Hlaing
4. Shugaban kasar Syria, Bashar Al-Assad
5. Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro
6. Shugaban Taliban na Afghanistan, Hibatullah Akhundzada
Menene Dalilin Kin Gayyatarsu
Bayanai sun nuna dalilan da yasa ba'a gayyaci wadannan shugabannin kasashe uku ba.
A farko Rasha: Alaka ta difilomasiyya dake tsakanin Birtaniya da Rasha ya yi tsami a shekarun baya-bayan sakamakon yakin dake gudana yanzu tsakanin Rasha da Ukraine
Bayan ga haka Vladimir Putin ba shi da niyyar halartar jana'izar, cewar mai magana da yawun sa.
Shi kuwa shugaban Belarus alakarsa da Vladimir Putin ce ta shafa masa bakin fenti wajen Birtanita. Aleksandr Lukashenko, aboki ne kut da kut na Shugaba Putin.
Game da Myanmar kuwa, Birtaniya ta yanke wata alaka da kasar Myanmar tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Aung Syu Kyi a watan Fabrairun 2021.
Jerin Shugabannin Kasan Da Aka Gayyata Jana'izar Sarauniya Elizabeth, Akwai Buhari
Daga cikin wadanda aka gayyata akwai sarakuna da shugabannin kasa.
Cikin Sarakuna, akwai Sarkin Belgium Philippe da Sarauniya Mathilde, Sarkin Netherlands Willem-Alexander da matarsa, Sarauniya Maxima da kuma Sarki Felipe da Sarauniya Letizia na Sifaniya
Asali: Legit.ng