Bayan Kwanaki 186 da Sace Fasinjojin Jirgin Kasa, Mutum 23 Suka Rage Hannun 'Yan Ta'adda
- Bayan kwanaki 186 da sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, har yanzu mutum 23 na hannun 'yan ta'adda
- An gano cewa, tun bayan da DSS suka kama Tukur Mamu, an gano cewa 'yan uwan fasinjojin basu sake ganawa da su ba
- Daya daga cikin 'yan uwan fasinjojin ya sanar da cewa, sun fawwalawa Ubangiji lamaurransu da fatan 'yan uwansu su dawo gida lafiya
Kaduna - Ashirin da uku daga cikin fasinjojin harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna suna hannun 'yan ta'adda bayan kwanaki 186 da sace su.
Daily Trust ta rahoto cewa, sama da fasinjoji 60 ne aka sace a farmakin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna.
Da yawa daga cikin fasinjojin da aka saki sun biya N100 miliyan wanda ake zargin mawallafin Kaduna, Tukur Mamu ya kai wa 'yan bindigan.
A makon da ya gabata ne hukumar tsaron farin kaya suka kama Mamu kan zarginsa da alaka da 'yan ta'adda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta tattaro cewa, tun bayan kamen Mamu, sauran dake hannun 'yan ta'addan basu sake ganawa da 'yan uwansu.
Mohammed Sabiu Barau wanda kaninsa 'dan hidimar kasa ne dake hannunsu, ya sanar da Daily Trust cewa sun bar su a hannun Ubangiji.
Kamar yadda yace, a matsayinsu na 'yan uwansu, a kullum suna fatan ganin ranar da za a sako su kuma su dawo gida.
"Muna cikin firgici a kowacce rana amma a matsayinmu na Musulmai, muna fatan sake ganinsu. Muna fatan samun taimakon Allah. A kowacce rana, muna fatan sake ganin sun dawo gida amma ba mu ji daga wurinsu ba har yanzu.
“Amma abinda muka ji a cikin kwanakin nan shi ne gwamnati ta saka kwamiti domin duba lamari kuma ana yin wani abu a kai, don haka muna fatan alheri."
- Yace.
'Yan Ta'addan Boko Haram Kasurguman 'Yan Damfara ne, Shugaba Buhari
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya bayyana ‘yan ta’addan Boko Haram a matsayin ‘yan damfara da gwamnatinsa ta durkusar tun a shekarar 2015.
Channels TV ta rahoto cewa, Buhari ya yi wannan batu ne a Owerri, babban birnin jihar Imo yayin da Gwamna Hope Uzodimma ya karba bakunsa bayan ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin ta yi.
Shugaban ya zargi jiga-jigan kasar nan da rashin dubawa Najeriya, inda ya kara da cewa duk da cewa gwamnatinsa ta yi matukar aiki tukuru, wadanda ya kamata su yaba wa nasarorin gwamnatinsa sun ki yin magana.
Asali: Legit.ng