Katsina: Yadda Rugugin Ruwan Kankara Ya Lalata Gonakin Jama'a
- Gagarumin rugugin ruwan kankara ya lalata sama da gonaki 300 na manoma a Dutsen Kura da Kanya da Gozaki
- Wasu mazaunan Gozaki sun bayyana cewa, ruwan saman mai kankara ya lalata gonakinsu, rufin gidaje da gilasan motoci
- Garuruwan da lamarin ya shafa sun hada da: Gidan Danwada, Gidan Sabo, Kabalawa, Unguwar Tsamiya, Dandabo, Unguwar Maigarma da sauransu
Katsina - Wata gagarumar ruwan kankara ya lalata gonaki da gidajen jama'a a yankunan Dutsen-Kura/Kanya da Gozaki a karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.
Malam Abdullahi Gozaki, wani mazaunin garin Gozaki ya sanar da Daily Trust cewa babu wani mutum daya da ya taba fuskantar irin wannan lamarin a yankin.
Yace gonakinsu, rufin gidaje da gilasan motoci duk suna lalace sakamakon ruwan kankarar da aka yi na tsawon mintuna.
Ya jero yankunan da lamarin ya shafa kamar haka: Gidan Danwada, Gidan Sabo, Kabalawa, Unguwar Tsamiya, Dandabo, Unguwar Maigarma, Uguwar Wanzamai da Unguwar Fulani.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A yayin tsokaci kan faruwar lamarin, shugaban karamar hukumar Kafur, Alhaji garba Kanya, yace kankarar ta lalata sama da gonaki 300 a yankuna da dama.
Yace da yawan amfanin gonakinsu na miliyoyin naira wadanda suka hada da masara, dawa, shinkafa, waken soya, albasa da barkono, duk sun lalace inda ya kara da cewa:
"A wasu gonakin, shinkafar su duk dun isa girbi."
Ya kara da cewa, hukumomin da suka dace daga ciki akwai Hukumar kula da aikin noma da raya karkara, KTARDA da hukumar kula da tallafiin gaggawa, SEMA, duk an sanar da su yawan barnar.
Katsina: Yadda Yarinya Mai Shekaru 13 Ta Haddace Qur'ani, Ta Rubuta shi da Hannunta
A wani labari na daban, wata yarinya mai shekaru 13 mai suna Zuwaira Ahmed dake kauyen Kagara dake karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina ta haddace tare da rubuta Qur'ani cikakke.
A yayin jawabi a taron da aka shirya domin karrama yarinya a ranar Asabar, Dagacin Mahuta, Bello Abdulkadir, ya bayyana jin dadinsa da farin cikinsa kan wannan cigaban, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.
Ya yi bayanin cewa wannan babban cigaba ne da aka samu a yakin da jihar baki daya balle a fannin ilimin addinin Islama.
Asali: Legit.ng