Shin Dagaske Tukur Mamu Ya Fallasa Sunayen Masu Daukar Nauyin Yan Ta'adda? Gaskiya Ta Fito

Shin Dagaske Tukur Mamu Ya Fallasa Sunayen Masu Daukar Nauyin Yan Ta'adda? Gaskiya Ta Fito

Tsohon mai ba da shawara kan tsaro (NSA), Janar Aliyu Gusau da tsohon gwamnan Sakkwato, Attahiru Bafarawa, na cikin sunayen da wani rubutu ya yi zargin Tukur Mamu ya ambata a matsayin masu ɗaukar nauyin 'yan ta'adda.

Rubutun dai ya yi ikirarin cewa Tukur Mamu, mai shiga tsakanin yan ta'addan da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna, ya fallasa wasu manyan mutane dake ɗaukar nauyin ta'addanci a arewacin Najeriya.

Rahoton ya kafa hujja da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a matsayin asalin labarin kuma ya watsu a Facebook da wasu kafafen sada zumunta na zamani.

Tukur Mamu.
Shin Dagaske Tukur Mamu Ya Fallasa Sunayen Masu Daukar Nauyin Yan Ta'adda? Gaskiya Ta Fito Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro cewa labarin ya ja ra'ayin mutane da dama a dandalin Facebook kuma an tura shi sama da sau 100 zuwa yanzun da muke haɗa muku wannan rahoton.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Shiga Wata Matsala, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Koma Bayan Gwamna Wike

Haka nan kuma labarin ya yi ikirarin cewa Mamu ya fasa ƙwan ne yayin da dakarun hukumar DSS ke bincikarsa. Wasu kafafen yaɗa labarai sun ɗakko rahoton.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Daga cikin waɗan da Mamu ya ambata sun haɗa da, tsohon NSA Janar Aliyu Gusau, tsohon gwamnan Sakkwato, Attahiru Bafarawa, da wasu Malaman Addini (ba'a faɗi sunayensu ba sai nan gaba kaɗan," a cewar labarin.

Menene gaskiyar wannan rahoton?

Domin tabbatar da sahihancin labarin, Daily Trust ta tuntuɓi babban Editan NANS, wanda ya shaida cewa labarai ba daga hukumarsu ya fito ba. Bugu da ƙari da muka bincika shafin NANS, sam basu buga labarin ba.

Daɗin daɗawa, mai magana da yawun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Peter Afunanya, abinda yace kaɗai shi ne sakamakon binciken da suka gudanar kan Tukur Mamu yana da ɗaure kai.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wani Abu Ya Fashe da Mutane, Ya Yi Mummunar Ɓarna a Jihar Jigawa

Sai dai bai bayyana ko sunan mutum ɗaya ba kamar yadda rubutun da ake yaɗa wa a Facebook ya yi iƙirari.

Kazalika ya kamata mutane su sani cewa babu wata sahihiyar kafar watsa labarai data ɗauki rahoton ta saka a shafinta na Intanet ko kuma wanda ake buga wa a takardu.

Idan baku manta ba a makon da ya gabata aka damƙe Tukur Mamu a birnin Cairo na ƙasar Masar yayin da yake kan hanyar zuwa Saudiyya yin Umrah tare da wasu iyalansa.

Daga nan aka taso shi zuwa Najeriya domin ya amsa tambayoyi masu alaƙa da zargin yana da hannu a ayyukan yan fashin daji da ta'addanci.

Rufewa

Legit.ng Hausa ta tabbbatar da cewa ikirarin cewa Tukur Manu ya ambaci Janar Aliyu Gusau da tsohon gwamna, Attahiru Bafarawa a matsayin masu rura wutar ta'addanci ƙarya ce.

Daga ƙarshe, an gudanar da wannan binciken gano gaskiyar ne bisa haɗin guiwar cibiyar raya Demokaraɗiyya (CDD).

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Bude Wuta, Sun Yi Garkuwa da Yayan Ɗan Takarar Gwamna Na PDP a Arewa

A wani labarin kuma kun ji cewa Kotu ta amince wa Hukumar DSS ta cigaba da rike Tukur Mamu na tsawon kwanaki 60

Hukumar DSS ta shigar da kara kotu don a bata daman cigaba da rike Tukur Mamu don kammala bincike.

Jami'an hukumar DSS sun tsare Tukur Mamu a hannun tun makon da ya gabata kan wasu zarge-zarge.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262