An Biya Matasa 2 Kudi N2000 Don Kashe Wani Tsoho A Jihar Adamawa

An Biya Matasa 2 Kudi N2000 Don Kashe Wani Tsoho A Jihar Adamawa

  • A jihar Adamawa, an damke wadannan matasan biyu kan laifin kashe wani tsoho a cikin gidansa
  • Hukumar yan sanda ta kaddamar da bincike kansu kuma an gano wata mata ta basu kudi su aikata hakan
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar Nguroje ya bayyana cewa ana neman matar da ta basu aikin ruwa a jallo.

Yola - An damke wasu matasa biyu a jihar Adamawa kan laifin kisan wani tsohon dan shekara 85 da adda.

Matasan masu suna Gayawan Danzaria dan shekara 22 da Thank-God Obadia dan shekara 18 dukkansu mazauna garin Shimba dake karamar hukumar Song ne suka aikata wannan kisa.

A cewarsu, wata mata ce ta basu aikin kashe tsohon saboda Maye ne kuma ya tsinewa 'danta, rahoton PMNews.

A cewarsu, sun bukaceta ta biya N5000 amma ta biyasu N2000 kuma tayi alkawarin basu cikon N3000 idan suka aikata kisan.

Kara karanta wannan

Adamawa: An biyashi N5000 da kwanon Shinkafa 4 don yayi kisan kai, ya kashe mutum 1, ya bar daya na jinya

Bayan haka Obadia ya dira cikin gidan misalin karfe 10 na safe bayan kowa ya fita kuma ya sassari marigayin a kai har lahira.

Shamba
An Biya Matasa 2 Kudi N2000 Don Kashe Wani Tsoho A Jihar Adamawa Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin hukumar yan sandan jihar SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce an damke matasan ranar Alhamis.

Nguroje ya bayyana cewa ana neman matar da ta basu aikin ruwa a jallo.

Yace:

"Matar da ta shirya kisan ta gudu yanzu kuma ina tabbatar muku muna kokari kuma za'a kama ta."

Adamawa: An Biyashi N5000 Da Kwanon Shinkafa 4 Don Yayi Kisan Kai, Ya Aikata

A wani labarin mai kama da wannan, hukumar yan sandan jihar Adamawa na neman wanda aka baiwa kwangilan kashe Amarya da Ango ruwa a jallo.

Mutumin mai suna Ibrahim Savanna ya aikata aika-aikan ne bayan biyansa kudi N5000 da kwanon shinkafa hudu.

Kara karanta wannan

Ta Yaudareshi Bayan Kashe Mata N150,000 Ta Auri Wani: Mutumin Yola Ya Bankawa Amarya Da Ango Wuta

Bayan karban kudin da shinkafar, Ibrahim Savanna, ya bankawa gidan amarya wuta cikin dare.

Wani mutumin jihar Adamawa, Ibrahim Muhammadu, ne ya bashi aikin bankawa Amarya da Ango wuta saboda matar ya yaudaresa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel