Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Maka ASUU A Kotu Bayan Sun Gaza Cimma Matsaya A Tattaunawarsu

Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Maka ASUU A Kotu Bayan Sun Gaza Cimma Matsaya A Tattaunawarsu

  • Gwamnatin tarayya ta garzaya kotu bayan ta gaza cimma masalaha tsakaninta da kungiyar malaman jami'a ta ASUU
  • Ministan kwadago, Chris Ngige, ya bukaci kotun masana'antu ta kasa da ta gaggauta sauraron shari'ar domin kawo karshen yajin aikin da ya ki ci yaki cinyewa
  • Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu ne malaman jami'a suka tafi yajin aiki kuma sun ce ba za su janye ba har sai an biya masu bukatunsu

Abuja - Ministan kwadago da daukar ma’aikata, Chris Ngige, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar maka kungiyar malaman jami’a ta ASUU a kotu saboda an kasa cimma matsaya daya tsakanin bangarorin biyu.

Jaridar The Sun ta rahoto cewa za a fara sauraron shari'ar ne a ranar Litinin, 12 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Allah-wadai: Rikici ya barke tsakanin Mali da Cote D'Ivoire, Buhari ya sha alwashin warwarewa

Kotun masana'antu ta kasa
Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Ta Maka ASUU A Kotu Bayan Sun Gaza Cimma Matsaya A Tattaunawarsu Hoto: The Sun
Asali: UGC

Batun zuwa kotun ya taso ne yan kwanaki bayan gwamnatin tarayya ta sanar da yiwa malaman jami’ar karin albashi da kuma alkawarin sama masu naira biliyan 150 a cikin kasafin kudin 2023 a matsayin kudaden farfado da jami’o’in gwamnatin tarayya, Daily Trust ta rahoto

Ministan ilimi, Adamu Adamu, wanda ya sanar da hakan a yayin taron shugabannin jami’o’in tarayya a ranar Talata, ya ce gwamnati ba za ta sa hannu a kowani yarjejeniya da ba za ta iya aiwatarwa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Adamu ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi tawagar gwamnati da ke tattaunawa da ASUU kan kulla yarjejeniyar da gwamnati ba za ta iya cikawa ba.

Sai dai kuma sanarwar karin albashi da ministan ya yi bai yiwa malaman jami’ar ba inda suka yi watsi da shi.

Ngige, a cikin wata wasika da ya aikewa babban magatakardar kotun masana’antu na Najeriya, Abuja mai kwanan wata 8 ga watan Satumba, ya bukaci kotun da ta gaggauta sauraron shari’ar domin kawo karshen yajin aikin.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Buhari ya amince a karawa lakcarori wani kason albashi, amma ASUU ta tubure

Daily Trust ta kuma rahoto cewa kotun ta samu wasikar a ranar 9 ga watan Satumba.

Wasikar ta ce:

“Duba da ganin cewa mambobin ASUU sun shiga yajin aiki tun a ranar 14 ga watan Fabrairu, sannan sun ki janye yajin aikin duk da tsoron abun da hakan zai haifar, zai kyautu idan aka gaggauta sauraron wannan takaddama domin kawo karshen rikicin.”

Ministan ya ci gaba da cewa, wannan mataki da ya dauka ta yi daidai da ikon da sashe na 17 na dokar takaddamar ciniki ya basa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng