Jigon Jam'iyyar PDP a Jihar Bayelsa Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Rasu a Asibiti

Jigon Jam'iyyar PDP a Jihar Bayelsa Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Rasu a Asibiti

  • Shugaban hukumar kula da tsaftar muhallai ta jihar Bayelsa, Mista Tolu Amatu, ya rigamu gidan gaskiya da daren Asabar
  • Wata majiya ta bayyana cewa ya fara ciwon ƙafa zuwa kugu da ciki, ya yanke jiki ya faɗi, ana kan hanyar Asibiti ya cika
  • A zamanin rayuwarsa, Amatu ya nemi takarar ɗan majalisar tarayya daga jihar Bayelsa amma ya sha ƙasa

Bayelsa - Shugaban hukumar tsaftace muhalli ta jihar Bayelsa, Mista Mr Tolu Amatu, ya riga mu gidan gaskiya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Bayanai sun ce Amatu, ya yanke ciki ya faɗi ba zato da daren ranar Asabar a gidansa dake kusa da Titin Baybrdge a yankin Kpansia, Yenagoa, babban birnin jihar.

Sai dai an ce an garzaya da shi Asbiti domin kulawa da lafiyarsa amma likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wani Ɗan Takarar PDP Daga Jihar Arewa a Zaɓen 2023 Ya Rasu

Mr Tolu Amatu.
Jigon Jam'iyyar PDP a Jihar Bayelsa Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Rasu a Asibiti Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Amatu, na ɗaya daga cikin yan takarar da suka gwabza neman tikitin mamba mai wakiltar mazaɓar Sagbama/Ekeremor a majalisar dokokin tarayya karkashin inuwar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayi tsohon shugaban hukumar tsaftace muhallin yana ɗaya daga cikin waɗan da suka yi murabus daga muƙamansu domin tsayawa takara a zaɓen fidda gwanin PDP.

Amma daga baya gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya mayar da su kan mukamansu bayan sun sha kaye a zaɓen.

Yadda lamarin ya faru

Wata majiya kusa da iyalan Mamacin ta bayyana cewa Marigayin ya yi korafin ƙafarsa na masa ciwo ranar Jumu'a kuma ya sha magani a gida ba tare da zuwa Asibiti ba.

Majiyar ta ƙara da cewa ya kuma koka kan kugunsa na masa ciwo da ciwan ciki washe gari ranar Asabar, daga baya ya fita domin zuwa ya biya ma'aikatan Otal ɗinsa Albashinsu.

Kara karanta wannan

2023: Hanya Ɗaya Da Zamu Kawo Karshen Rikicin Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar Ya Magantu

Ya yanke jiki ya faɗi a gidansa kuma aka yi gaggawar kai shi wani Asibiti dake kan Titin Saptex, a birnin jihar, da dare Likitoci suka tabbatar da ya mutu.

Mutumin yace, "Ya yi korafin ƙafarsa na masa ciwo ya sha magani, jiya kuma yace cikinsa na masa zafi, ya zagaya bayan gida. Nan aka ba shi shawarin ya sha lemu da wasu abubuwa kuma ya sha."

"Ya kwanta domin ya huta daga baya ya tafi Otal domin ya biya ma'aikata albashi wajen karfe 5:00 na yamma. Lokacin da ya dawo gida ya hau Bene kawai sai ya faɗi. Abun bakin ciki ya rasu tun kafin akm a isa Asibiti."

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, gwamnatin jihar Bayelsa ba ta fitar da sanarwa a hukumace game da mutuwar shugaban hukumar tsaftace muhalli ba.

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Bude Wuta, Sun Yi Garkuwa da Yayan Ɗan Takarar Gwamna Na PDP a Arewa

Kara karanta wannan

"Dole Ya Sauka" Gwamna Wike Ya Maida Zazzafan Martani Ga Majalisar Koli Ta PDP Kan Ayu

'Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun yi awon gaba da babban yayan ɗan takarar PDP da ya nemi tikitin gwamna a jihar Filato.

Mazauna yankin sun tabbatar da faruwar harin ranar Asabar, sun ce maharan sun nemi a tattara musu miliyan N100m na fansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: