Abba Kyari Bai Da Wata Gungun Masu Kashe Mutane, Karya Hushpuppi Ke Masa: Lauyansa

Abba Kyari Bai Da Wata Gungun Masu Kashe Mutane, Karya Hushpuppi Ke Masa: Lauyansa

  • Lauyan Abba Kyari ya karyata jawabin da Hushpuppi ya yiwa kotun Amurka cewa yana da wata gungun makasa a Najeriya
  • Hushpuppi ya roki kotun Amurka kada a mayar da shi Najeriya saboda Abba Kyari zai kasheshi
  • Abba Kyari yanzu haka yana tsare da kurkukun Kuje bisa zargin hannu wajen safarar hodar iblis

Suleiman Mohammed, Lauyan Dakataccen mataimakin kwamishanan yan sanda DCP Abba Kyari ya karyata maganar cewa wanda yake karewa a kotu na da wata gungun makasa a Najeriya, rahoton TheCable.

An dakatad da Abba Kyari daga hukumar yan sanda bisa alakarsa da Abbas Ramon Hushpuppi, dan damfaran da aka kama a Dubai.

HushKyari
Abba Kyari Bai Da Wata Gungun Masu Kashe Mutane, Karya Hushpuppi Ke Masa: Lauyansa
Asali: Facebook

Lauyan ya bayyana hakan ne a martanin da yayi kan rahotannin da ke yaduwa cewa Hushpuppi ya bayyanawa kotun Amurka cewa Abba Kyari zai kashehi idan ya dawo Najeriya.

Kara karanta wannan

Kada Ku Mayar Dani Najeriya, Abba Kyari Zai Iya Kasheni: Hushpuppi Ya Roki Kotun Amurka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Suleiman yace babu ruwan Abba Kyari da Hushpuppi kuma basu taba harkalla ba.

A jawabin da ya fitar, yace:

"Ina martani ne saboda in bayyanawa jama'a dake tunanin shirun da Abba Kyari ke yi tsarguwa ne kan karyar da aka mai."
"Da farko, ta yaya babu wanda ya taba samun labarin wata gungun makasa sai yanzu da wani dan iska ke neman sauki gaban kotu? Shin irin wannan mutumi ya mai neman rangwame ya kamata a gaskata?
"Hushpuppi ya kawo kansa wajen Kyari ta hannun wani Yomi lokacin Kyari da ya kai ziyara Dubai da iyalansa a 2019. Wannan shine karon farko da Kyari ya hadu ido da ido da Hushpuppi."

Kada Ku Mayar Dani Najeriya, Abba Kyari Zai Iya Kasheni: Hushpuppi Ya Roki Kotun Amurka

Jiya kun ji cewa shahrarren dan damfarar yanar gizo, Ramon Abbas, wanda akafi sani da Hushpuppi ya ce dakataccen dan sanda Abba Kyari na iya kasheshi idan gwamnatin Amurka ta mayar da shi Najeriya.

Kara karanta wannan

Allah-wadai: Rikici ya barke tsakanin Mali da Cote D'Ivoire, Buhari ya sha alwashin warwarewa

A cewar Peoples Gazette, Hushpuppi ya bayyanawa kotun birnin California cewa tona asirin Abba Kyari da yayi ba karamin hadari ne ga rayuwarsa ba yanzu idan ya koma Najeriya bayan zama a gidan kurkuku a Amurka.

Wannan na kunshe cikin takardar da ya gabatar gaban Alkali Otis Wright inda yake rokon a rage adadin shekarun da ake shirin yanke masa na zaman Kurkuku.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida