An Bayar da Belin Mawakin Najeriya Ice Prince, Kotu ta Saka Ranar Cigaba da Shari'a

An Bayar da Belin Mawakin Najeriya Ice Prince, Kotu ta Saka Ranar Cigaba da Shari'a

  • An sakon mawakin gambara 'dan Najeriya, Ice Prince, daga gidan gyaran halin Ikoyi bayan ya cika sharuddan belinsa
  • An gurfanar da mawakin a gaban kotu a makon da ya gabata bayan an zargesa da cin zarafin 'dan sanda tare da garkuwa da shi
  • Mawakin ya cika sharuddan belin da aka gindaya masa inda aka dage sauraron shari'ar zuwa ranar 24 ga watan Oktoba

Legas - Mawakin gambaran Najeriya Ice Prince, an sako shi da gidan gyaran hali dake Ikoyi dake jihar Legas bayan cika sharuddan belinsa.

Fitaccen mawakin yana fuskantar kotun majistare dake Ajah a kan zargin aikata laifuka uku da suka hada da zargin cin zarafi, hana 'dan sanda yin aikinsa da kuma garkuwa da mutum.

Mawaki Ice Prince
An Bayar da Belin Mawakin Najeriya Ice Prince, Kotu ta Saka Ranar Cigaba da Shari'a. Hoto daga tvcnews.tv
Asali: UGC

Ice Prince, wanda asalin sunansa Panshak Zamani, 'yan sandan jihar Legas sun kama shi a ranar 2 ga watan Satumba, TVC ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mutum 43 Da Aka Sace A Masallacin A Zamfara Sun Samu Kubuta Bayan Biya Kudi, Daya Ya Mutu

Kakakin rundunar 'yan sandan, Benjamin Hundeyin, yace a lokacin da mawakin ya ci zarafin 'dan sandan, ya yi barazanar wurga shi cikin ruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gurfanar da shi a ranar Juma'a da ta gabata kuma kotun tun farko ta amince da bada belinsa kan kudi N500,000 sannan ya samar da tsayayyu biyu.

Kotun ta bayar da umarnin garkame shi a gidan gyaran halin Ikoyi har sai ya cika sharuddan beli.

A yayin da aka cigaba da shari'ar a ranar Laraba, lauyan masu kara sun bukaci kotu da ta dage sauraron shari'ar saboda rashin zuwan masu bada shaida biyu zaman kotun.

A yayin zaman kotun, Folarin Dalmeida, wanda shi ne lauyan mawaki, ya gabatar da tsayayyun biyu kamar yadda kotu ta bukata a matsayin sharadin belin.

Daga bisani an mayar da Ice Prince gidan gyaran hali na Ikoyi har zuwa lokacin da za tantance tsayayyn biyu.

Kara karanta wannan

Ke duniya: An kama wata malamar coci dake sayen yara kanana kan kudi N50,000

Lauyan wanda ake karar daga bisani ya sanar da TVC cewa an saki Ice Prince daga bisani a ranar Alhamis wurin karfe 3 na yamma. An dage sauraron shari'ar zuwa ranar 24 ga watan Oktoba.

Jarabar Mijina ta Ishe ni, Neman Hakkinsa Yake da Azumi ko Ina Al'ada, Matar Aure ga Kotu

A wani labari na daban, wata matar aure mai suna Zainab Yunusa ta bukaci kotun shari'a dake zama a Magajin Gari, Kaduna, ta ta tsinke igiyar aurenta da mijinta mai suna Alhaji Ali garba Ali saboda tsabar jarabarsa.

Daily Trust ta rahoto, mai karar a ranar laraba ta sanar da kotu cewa Garba na neman jima'i ko a lokutan da take al'adan da lokacin azumin watan Ramadan.

Zainab tace sun yi zaman aure na shekara daya kacal inda ta kara da cewa ta bar gidansa ne saboda wannan lamarin.

Wacce ke karar ta yi bayanin cewa a yayin zamansu, Garba ya saba dawowa gida har da rana a lokutan da take jinin al'ada don ya kwanta da ita, wanda addinin Islama bai aminta da hakan ba.

Kara karanta wannan

Rivers: N50,000 Na Siya Kowanne Daga Cikinsu: Rabaren Sista da Aka Kama da Yara 15

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: