Dalilin Da Ya Sa Koma Makarantar Da Nayi Digiri Nace Su Dawo Min Da Kudi Na
- Sabon bidiyon matashin da ya koma jami'ar da ya kammala digiri yace a bashi kudinsa ya bayyana
- A faifain bidiyon, matashin ya bayyana irin keburan da ya sha sakamakon rashin aikin yi tun bayan kammala karatu
- A cewarsa, shekaru tara kenan da kammala karatun ilimin aikin noma a jami'ar LAUTECH, Ogbomosho
Wani matashi mai suna Oludare Alaba ya bayyana cewa shine mutumin da aka gani cikin bidiyo ya je jami'ar fasahar Ladoke Akintola University (LAUTECH) ya tada tarzoma.
Legit ta kawo muku labarin wannan matashi da ya shiga makarantar da ya kammala karatun digirinsa inda ya bukaci su amshi kwalinsu su dawo masa da kudaden makarantar da ya biya tsawon shekarun da yayi a jami'ar.
Kwana daya bayan bayyanar bidiyon, wani sabon bidiyo ya bayyana inda Oludare Alaba ya fadi dalilin da ya sa ya koma jami'ar.
Alaba yace ilmin aikin noma ya karanta kuma ya kammala tun 2015 amma har yanzu babu aikin yi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa:
"Na karbi kwali ne amma bata amfanar da ni komai ba. Na ji kebura a rayuwar nan amma dama daya dana samu shine inyi asirin kudi amma ba zan yi ba."
"Na bukaci mahaifi ne ya taimaka min da wasu kudade don in nemi abin yi. Ni dan wasan nishadi ne. Na samu lambobin girma da dama lokacin bautar kasa NYSC a 2016. Amma yace min bashin da ya karba don biyan kudin makarantana har yanzu bai gama biya ba."
"Wata rana har ce min yayi da yiwuwan idan suka mutu sai na karbi bashi zan iya jana'izarsu. Sai da nayi kuka ranar."
Har wa yauzu jami'ar ba tayi tsokaci kan wannan abu da ya faru ba.
Kalli bidiyon:
Shin me zai tursasa matashin yin haka
A farko shekarar nan, Statisa ta sakin rahoton rashin aikin yi tsakanin mata a 2022.
Rahoton ya nuna cewa alkaluman rashin aikin yi ya tashi daga 32.5% zuwa 33%.
Hakazalika a 2020, cibiyar kididdiga ta Najeriya NBS, tace kimanin masu kwalin doktora, 38,000 basu da aikin yi ko kuma suna ayyukan da bai kai matsayin mutuncinsu ba.
Matasan Najeriya kulli yaumin na guduwa zuwa kasashen wajen domin nemawa kans ayyukan yi.
Asali: Legit.ng