Atiku-Wike: Yau Alhamis Za'a Yanke Shawara Kan Cire Shugaban PDP, Iyorchia Ayu

Atiku-Wike: Yau Alhamis Za'a Yanke Shawara Kan Cire Shugaban PDP, Iyorchia Ayu

  • Majalisar Zartaswar jam'iyyar adawa ta PDP tana zama tun jiya don yanke shawara kan shugabanta Iyorchia Ayu
  • Rikici ya barke cikin jam'iyyar wanda ya ka zama mata matsala a zaben shugaban kasa a 2023
  • Shugaban PDP, Ayu, ya bayyana cewa jam'iyyar APC ke ruruta wutar rikicin dake faruwa a jam'iyyarsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Manyan masu fada a aji na Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kokarin kawo karshen rikicin dake kokarin barka lemar dake basu inuwa.

Kwamitin dattawan jam'iyyar da kwamitin NEC na jam'iyyar na zama tun ranar Laraba domin yanke shawara kan shin Iyorchia Ayu ya cigaba da zama shugaban bisa bukatar bangaren Wike ko kuma a tsigeshi.

TheNation ta ruwaito cewa jigogin jam'iyyar na tsoron idan ba'a magance wannan rikici ba, zasu fuskanci matsala a zabe.

Hakazalika daga cikin abubuwan da ake tattauna kansu a zaman shine lamarin kafa kwamitin yakin zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

PDP: Gaskiyar Dalilin Da Yasa Gwamnoni Suka Ki Zuwa Taron Jam’iyya A Abuja

Rikicin PDP
Atiku-Wike: Ranar Alhamis Za'a Yanke Shawara Kan Cire Iyorchia Ayu, Shugaban PDP Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Masu cewa in yi murabus yara ne lokacin da muka kafa PDP

Iyorchia Ayu, ya ce masu kira ga yayi murabus daga kujerarsa kananan yara ne basu nan lokacin da aka kafa jam'iyyar.

Gwamna Wike da mabiyansa ne ke kira ga Shugaban PDP, Ayu, yayi murabus a matsayin sharadin marawa takarar Atiku goyon baya.

Wannan abu ya hargitsa rikici a cikin babbar jam'iyyar ta adawa.

Alhaji Atiku Abubakar ya kayar da Wike a zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP.

Duk da an bukaci Atiku ya zabi Wike matsayin mataimaki, ya zabi gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa.

Masu goyon bayan Wike sunce ba zai yiwu dan takarar shugaban kasa da shugaban jam'iyya su kasance daga yankin Arewa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida