Sai Na Dirje Kafin Na Zabo Mijin Aure Don Ba Zan Taba Auren Talaka Ba, Inji Jarumar Fim
- Jarumar fim ta kasar Ghana, Xandy Kamel, ta sha alwashi cewa ba za ta sake auren mijin da bai amsa sunan mai kudi ba
- Kamel ta bayyana cewa sai ta bi salsala wajen gano dukiyar da mutum ya tara kafin ta yarda ta aure shi don ita da miji talaka sun yi hannun riga
- Ta bayyana cewa yawancin mazan da basu da kudi mugaye ne kuma basu san hallaci ba a rayuwa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Ghana - Shahararriyar jarumar kasar Ghana, Xandy Kamel, ta bayyana cewa ta yi nadamar auren tsohon mijinta mai suna Kaninja.
Da take zantawa da manema labarai, Kamel ta kuma ce ta yi danasanin auren namijin da bai da kudi da ya amsa sunansa kudi, shafin LIB ya rahoto.
Jarumar ta kuma bayyana cewa ta koyi darasi soasai a aurenta na baya inda ta sha alwashin cewa ba za ta sake auren mutumin da bashi da kudi ba. A cewarta yawancin mazajen da basu da kudi butulu ne kuma mugaye ne sosai.
Har ila yau, ta bayyana cewa sai tayi bincike tun daga tushe don tabbatar da ganin cewa mijin da zata sake aure a gaba yana da arziki saboda ta rufe babin shan wahala da namiji.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da aka nemi jin ta bakinta game da rade-radin cewa ita ce ta dauki nauyin aurenta, sai tace ta taimaka da kudadenta da take tarawa saboda ta zata tsohon mijin nata zai zamo miji nagari kuma mai daukaka a gaba tare da sanin cewa mafarki kawai take yi ba.
Jarumar ta kuma gargadi mazajen da basu ajiye komai ba da ke neman tayin aurenta da su yi ta kansu don ba za ta sake tafka kuskure irin na baya ba.
Ku Kama Mazajenku Da Kyau, Maza Tsada Suke A UK: Budurwa Da Ke Turai Ta Shawarci Yan Matan Najeriya
Bayan Shafe Shekaru 3 Tana Aiki A Kasar Waje, Budurwa Ta Dawo Gida Najeriya, Ta Zama Mai Jiran Shago
A wani labari na daban, wata matashiya yar Najeriya da ke zama a kasar waje ta yi bidiyo a TikTok, tana mai shawartan yan matan Najeriya a kan kada su zo Birtaniya da tunanin samun miji.
Ta bayyana cewa a UK, aiki shine mazajensu. Budurwar ta shawarci yan matan da ke Najeriya a kan su rike mazajensu da kyau.
Mutane sun je sashinta na sharhi don tabbatar da abun da ya fadi game da rayuwar aiki kurum da ake yi a UK.
Asali: Legit.ng