Kakakin Rundunar Yan Sandan Ribas Mafi Dadewa, Omoni, Ya Mutu
- Tsohon kakakin 'yan sandan jihar Ribas kuma DPO na Ofishin Elimgbu, Nnamdi Omoni, ya rasu a bacci ranar Talata
- Kwamishinan yan sandan jihar Ribas, Friday Eboka, ya mika sakon ta'aziyya ga iyalansa da sauran al'umma baki ɗaya
- Rahoto ya nuna cewa Mamacin ya yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa ranar Jumu'a da ta gabata
Rivers - Rundunar 'yan sanda reshen jihar Ribas ta shiga jimami biyo bayan mutuwar tsohon mai magana da yawun rundunar, Nnamdi Omoni, ta farat ɗaya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Omoni, ya rasu ne daga kwanciya bacci kuma an gano gawarsa a gidansa ranar Talata, 30 ga watan Agusta, 2022.
Wanda ta gaje shi kuma kakakin 'yan sandan jihar a yanzu, Grace Iringe-Koko, ita ce ta tabbatar da rasuwar a wani gajeren sako da ta aike wa wakilin jaridar cikin jimami.
Misis Iringe-Koko, tace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ina shirya sanarwa ga manema labarai a hukumance. Nan ba da jimawa ba zamu sake ta da zaran kwamishinan 'yan sanda ya amince."
Marigayi Omoni ya kasance kakakin yan sanda mafi daɗe wa a kan kujerar a jihar Ribas, bayanai sun ce ya kwashe shekaru biyar a kan muƙamin.
Jim kaɗan bayan kara masa matsayi zuwa SP, aka maida shi Hedkwatar 'yan sanda dake Elimgbu, ƙaramar hukumar Obio/Akpor, jihar Ribas a matsayin DPO na Ofishin.
A ranar Jumu'a da ta gabata Mamacin ya yi bikin ƙarin shekarunsa a Patakwal, babban birnin jihar tare da 'yan uwa, abokai da abokanan aikinsa na 'yan sanda.
Yadda ake ta'aziyyar mutuwar ɗan sandan
Kwamishinan yan sandan Ribas, Friday Eboka, ya yi ta'aziyyar rasuwar jami'in ɗan sandan a wata sanarwa da kakaki, Grace Iringe-Koko, ta fitar a hukumance.
Sanarwan ta ce:
"Marigayi SP wanda ya fito daga Ndele, yankin ƙaramar hukumar Emohua ya shiga aikin ɗan sanda ne a ranar 1 ga watan Nuwamba, 1989, ya yi aiki a wurare da dama ciki har ofishin PPRO na tsawon shekaru."
"Shi ne shugaban Ofishin Elimgbu kafin rasuwarsa, hukumar yan sanda na miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan Omoni, abokanai da baki ɗaya al'ummar jihar Ribas.
Haka nan, jam'iyyar APC ta hannun kakakinta, Darlington Nwauju, yace sun samu labarin rasuwar ɗan sandan cikin kaɗuwa, inda ya ƙara da cewa marigayin ya yi aiki yana maraba da kowa.
A wani labarin kuma kun ji yadda Matan Aure 2 Da Yaransu 5 Suka Mutu Bayan Yin Karin Kumallo A Sokoto
Mutanen kauyen Kaura da ke karamar hukumar Yabo ta Jihar Sokoto sun shiga jimamin rashin wasu mata 2 da yayansu biyar da suka rasu.
Rahotanni ya nuna cewa daya cikin matan ne ta dafa dambu dukkan yan gidan suka ci yayin karin kumallo amma daga bisani suka fara ciwon ciki wanda ya yi sanadin rasuwarsu.
Asali: Legit.ng