Yadda Budurwa Ta Zama Mai Goge-goge Bayan Kammala Digiri Na Biyu, Allah Ya Sauya Rayuwarta A Karshe

Yadda Budurwa Ta Zama Mai Goge-goge Bayan Kammala Digiri Na Biyu, Allah Ya Sauya Rayuwarta A Karshe

  • Wata budurwa da ta mallaki digiri har biyu amma bata samu aiki ba sai na goge-goge ta bayar da labarin sauyin da Allah ya kawo mata
  • Budurwar ta sadaukar da lokacinta ga Allah yayin da take koyawa yara littafi mai tsarki da yadda za su zama masu riko da addini
  • A cewarta, Ubangiji ya sauya labarinta a yanzu, ta samu aiki mai kyau kuma tana yin digiri dinta na uku

Wata matashiyar budurwa da ta gaza samun aiki mai kyau bayan kammala karatunta ta bayyana cewa ta shiga damuwa a saboda haka. Bayan dan wani lokaci, ta fara aiki a matsayin mai goge-goge duk da cewar tana da digiri biyu.

Daga nan sai ta fara koyawa wasu dalibai yadda za su yi addu’a da azumi. Budurwar tana kuma karantar da su darusa daga littafi mai tsarki.

Kara karanta wannan

Bayan Shafe Shekaru 3 Tana Aiki A Kasar Waje, Budurwa Ta Dawo Gida Najeriya, Ta Zama Mai Jiran Shago

Budurwa
Yadda Budurwa Ta Zama Mai Goge-goge Bayan Kammala Digiri Na Biyu, Allah Ya Sauya Rayuwarta A Karshe Hoto: TikTok/@apfe_gets_fit
Asali: UGC

Daga aikin goge-goge zuwa matakin nasara

Duk da wannan hali da take ciki da kuma kasancewarta mai goge-goge, ta yi tawakkali da Allah sannan ta ci gaba da koyar da kananan yara a hanya madaidaiciya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan dan wani lokaci, sai ta zama bai bayar da shawara kan ilimi a wata makarantar sakandare. Rayuwarta ta sauya gabaki daya a lokacin da ta samu aiki mai kyau a matsayin jami’ar muhalli. Ba a nan abun ya tsaya ba, yanzu tana karatun digiri dinta na uku.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

Ree Relebogile ta ce:

“Wannan irin kyakkyawan labara. Ya amsa da eh diyata. Ba yanzu ba, da fari an horar da ke don kada ki wofantar da albarkarki.”

Rishongile ta ce:

“An zabe ki ne don ki sauya rayuwar wadannan yaran ne.”

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 3 Da Aure Ba Tare Da Sun Ga Juna Ba, Yar Najeriya Ta Hadu Da Baturen Mijinta A Amurka

AndileNtsanwisi ta ce:

“Akwai aikin da za ki cika ne kafin ki fara rayuwar da kike mafarki kuma Allah ya amsa addu’ar. Wadannan yaran suna bukatar ceto fiye da yadda kike tsammani.”

Bayan Shafe Shekaru 3 Tana Aiki A Kasar Waje, Budurwa Ta Dawo Gida Najeriya, Ta Zama Mai Jiran Shago

A wani labarin, wata matashiyar budurwa ta je shafin soshiyal midiya don bayyana yadda tayi tawakkali duk da cewar rayuwa ta juya mata baya.

A cikin wani bidiyon TikTok, ta bayyana cewa bayan ta shafe shekaru uku a kasar Larabawa, ta dawo gida ta kama sana’ar bakin hanya, yanzu tana jiran shagon caca ne.

A yayin daukar bidiyon, an gano matar tana aiki a na’urar buga caca yayin da take taka rawa. Ta bayyana cewa duk da halin da take ciki, tana godiya ga Allah da ya barta da ranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng