Zargin Cire Koda: Da Alamu Ekweremadu Zai Dade A Gidan Yari, An Samu Sabon Cigaba
- An bukaci mai shari'a Iyang Ekwo na babban kotun tarayya a Abuja ya janye hukuncinsa na umurtar a sakin bayanan David Ukpo
- David Ukpo shine wanda ake zargin Sanata Ekweremadu da matarsa Beatrice sun tafi da shi Landan don cire masa koda
- Ana sa ran za a tura bayansa zuwa Landan ne don cigaba da shari'ar Sanata Ekweremadu
FCT Abuja - David Ukpo, wanda ake zargin an kai shi Landan don cire masa koda, ya roki babban kotun tarayya ta janye hukuncin da ta yi na tura bayanansa zuwa Landan don cigaba da shari'ar Sanata Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice.
Wani rahoto na Jaridar The Nation ta ce Ukpo, ta bakin lauyansa Bamidele Igbinedion ya koka cewa ba a saka shi ko Antonji Janar na Najeriya ba cikin karar da ya yi sanadin hukuncin na ranar 1 ga watan Yuli da Mai Shari'a Inyang Ekwo ya fitar.
Abin da karar Ukpo ta ce
Ukpo ya ce an keta masa hakkinsa na dan adam kuma ba a masa adalci ba wurin neman yardarsa a shari'ar da ta haifar da hukuncin babban kotun na Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sabon karar da Ukpo ya shigar, an saka hukumar NIMC, Kwantrola Janar na Hukumar Shige da Fice da wasu bankunan zamani cikin wadanda ake kara.
Ukpo yana bukatar babban kotun na Abuja ta hana wadanda ya yi karar duba bayanansa na sirri.
Safarar Sassan Jikin Mutum: Za A Iya Yi Wa Ekweremadu Da Matarsa Daurin Rai Da Rai A Birtaniya
A wani rahoton, kun ji cewa ta yi wu a yi wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice daurin rai-da-rai idan aka samesu da laifi kuma aka yanke musu hukunci mafi tsauri a dokar Birtaniya ta Modern Slavery Act, 2015 (MSA 2015).
An su ne aka kuma gurfanar da su a kotun Birtaniya kan zargin hannu cikin cire sassan dan adam a kotun Majistare da ke Uxbridge a ranar Alhamis.
Yan sandan Landan sun ce sun fara bincike kan mutanen biyu ne bayan jami'an tsaro sun ankarar da su kan laifukan karkashin dokar bautarwa na zamani a Mayun 2022.
Asali: Legit.ng