Adadin Mutanen da Suka Mutu a Ambaliyar Ruwan Jigawa Ya Karu Zuwa 51

Adadin Mutanen da Suka Mutu a Ambaliyar Ruwan Jigawa Ya Karu Zuwa 51

  • Al'umma na cigaba da aikin tsamo gawarwaki biyo bayan ibtila'in da ya faɗa musu na Mabaliyar ruwa a yankunansu a Jigawa
  • Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa (SEMA) ya ce zuwa yanzun adadin gawarwakin da aka tsamo ya kai 51
  • Sani Yusuf ya ce gwamnatin jiha na iya bakin ƙoƙarinta amma lamarin ya zarce karfinta, ta tura rahoto ga Buhari

Jigawa - Adadin rayukan da aka rasa a Ambaliyar ruwan jihar Jigawa ya ƙaru zuwa mutum 51 yayin da mazauna yankin ke cigaba da aikin ceto bayan ruwa ya fara janye wa.

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA), Sani Yusuf, shi ne ya bayyana haka ga Channels tv ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Sa Labule da Wasu Gwamnoni a Aso Rock, Hotuna

Ambaliyar ruwa a Jigawa.
Adadin Mutanen da Suka Mutu a Ambaliyar Ruwan Jigawa Ya Karu Zuwa 51 Hoto: channelstv
Asali: UGC

A cewarsa, kusan magidanta 2,051 ne suka rasa muhallansu a ƙauyen Karnaya, yankin Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Shugaban SEMA ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Gwamnatin jiha na shirye-shiryen tsugunar da iyaye mata 404 tare da 'ya'yansu 1,334 a sansanin 'yan gudun Hijira dake Warwade, yayin da Maza 313 zasu cigaba da zama a Filin makarantar Firamaren ƙauyen har lokacin da ruwan zai janye."

Lamarin ya fi ƙarfin gwamnatin jiha - SEMA

Mista Yusuf ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta aike da rahoton abinda ya faru ga gwamnatin tarayya, tana mai rokon tallafin yadda za'a magance ibtila'in.

"Mun tura rahoto zuwa ga gwamnatin tarayya saboda wannan matsalar ta fi ƙarfin mu, muna bukatar tallafi na gaske. A yanzu da nake zantawa da ku, ruwa na cigaba da cinye wasu garuruwa."
"Baya ga haka, gadoji da dama na cigaba da rushe wa, muna kira ga Direbobi da su kula yayin gudanar da aikinsu na tuki."

Kara karanta wannan

Insha Allahu Mijina Zai Lashe Zaɓen Gwamnan Bauchi a 2023, Ministar Buhari

A wani labarin kuma Za a yi Gagarumin Ruwan Sama na Tsawon Kwanaki 4 a Jihohi 6 na Najeriya inji hukumar NiMet

Hukumar hasashen yanayi ta NiMet ta sanar da cewa za a yi gagarumin ruwan sama a jihohin arewa 6 a cikin kwanaki hudu.

Kamar yadda ta bayyana, jihohin Kaduna, Niger, Bauchi, Filato, Nasarawa da babban birnin tarayya ne zasu fuskanci ruwan mai yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262