Dan Shekaru 71 Ya Koma Makarantar Firamare, Bidiyo Ya Nuno Sa A Aji Tare Da Jikokinsa
- Wani tsohon soja mai shekaru 71 ya koma makarantar firamare don kammala karatunsa da ya bari sannan ya shiga aikin soja
- Tsohon mai suna Isaac yana zuwa makaranta tare da jikokinsa kuma wani bidiyo da aka gano a Youtube ya nuno sa a aji
- Isaac ya ce lallai iliminsa zai yi masa amfani duk da tsufansa kuma mahaifiyarsa ta ce ta yi farin ciki da komawarsa makaranta
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Tanzaniya - Labarin wani tsoho mai shekaru 71 wanda ya koma makaranta don samun ilimi ya burge mutane da dama a yanar gizo.
Tsohon mai suna Isaac ya kasance tsohon soja wanda bai kammala karatunsa ba kafin ya shiga rundunar sojojin.
Bayan ya yi ritaya, mutumin dan kasar Tanzaniya ya yanke shawarar komawa makaranta bayan ga cewa takwarorinsa sun yi masa nisa a bangaren ilimi.
Sarkin Kiriniya: Yadda Karamin Yaro Ya Bi Ya Bata Wajen Da Mahaifinsa Ya Gyara, Bidiyon Ya Kayatar Da Mutane
Ilimina zai mani amfani
Isaac ya dage sai ya kammala karatunsa kuma ya ce zai yi masa amfani, tsufa ba zai zama shamaki ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mahaifiyarsa na matukar farin ciki cewa danta ya yanke shawarar komawa makaranta duk da cewar tare da jikokinsa yake zuwa.
A wani bidiyo da Afrimax English ya wallafa a YouTube, an gano mutumin a cikin aji tare da abokan karatunsa wadanda suka ce suna farin ciki da samunsa a tsakaninsu.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Carol Strange ya yi martani:
"Isaac kada ka bari wani ya sanyaya maka gwiwa aikinka na kyau Isaac Allah ya albarkace ka da iyalinka da jikokinka."
Reina Macaren-a ta ce:
"Bai yi kama da dan shekaru 71 ba. Idan ka daina karatu ka daina rayuwa. Amincin Allah su tabbata a gareka Isaac."
Shola Pedro ta yi martani:
"Mahaifiyarsa na da kyau da karfi har yanzu, wannan alfarma ce daga Allah."
Har Yanzu Sabo Fil Nake: Bidiyon Tsoho Dan Shekaru 90 Wanda Bai Taba Yin Budurwa Ko Mata Ba
A wani labarin kuma, wani tsoho dan shekaru 90 mai suna Baizirre Jean Marie ya bayyana cewa har yanzu a kasuwa yake baida aure.
Kafar labarai ta Afrimax English ta ziyarci kauyen mutumin kuma sun zanta da shi, inda ya bayyana matsayinsa a soyayya.
Baizire ya bayyanawa kafar labaran cewa ya tsaya ne a aji biyar na makarantar firamare, wanda yace bai tsinana masa komai ba.
Asali: Legit.ng