Hukumar DSS Ta Sako Fitacciyar Mai Goyon Bayan Ƙungiyar IPOB, Mama Biafra

Hukumar DSS Ta Sako Fitacciyar Mai Goyon Bayan Ƙungiyar IPOB, Mama Biafra

  • Hukumar DSS ta ƙasa ya saki, Ukamaka Ejezie, wacce aka fi sani da Mama Biafara, mahaifiyar Nnamdi Kanu daga tsare
  • Shugabar tawagar lauyoyin Kanu, Ifeanyi Ejiofor, shi ne ya tabbatar da haka, ya ce zasu yi duk me yuwuwa su fitar da kowa
  • Jami'an tsaro sun yi ram da matar ne a zaman Kotu da Kanu ya halarta na baya-bayan nan a watan Mayu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Bayan shafe makonni a magarƙama, fitacciyar mai goyon bayan haramtacciyar ƙungiyar ƴan aware IPOB, Ukamaka Ejezie, wacce aka fi sani da Mama Biafara, ta samu yanci daga hannun jami'an tsaro.

Punch ta ruwaito cewa Mama Biyafara ta ɗauki shugaban IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, tamkar ɗan da ta haifa kuma an sako ta ne ranar Lahadi.

Hukumar DSS.
Hukumar DSS Ta Sako Fitacciyar Mai Goyon Bayan Ƙungiyar IPOB, Mama Biafra Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shugaban tawagar lauyoyin da ke kare Kanu, Ifeanyi Ejiofor, shi ne ya tabbatar da sako matar a wata sanarwa da jaridar Punch ta ci karo da ita.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Allah Ya Yiwa Sarkin Funukaye, Alhaji Muhammad Muazu Kwaranga, rasuwa

Ya ce, "Ina farin cikin sanar da ku cewa Misis Ukamaka Ejezie (Mama Biafra) ta samu yanci, yanzu ta fito daga magarƙamar hukumar DSS. Godiya ga Chukwuokike Abiama, bisa wannan nasara."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba zamu huta ba duk wanda yake zaman Fursun kan wannan lamarin, har da wanda muke kare wa, Onyendu Mazi Nnamdi, ba da jima wa ba zasu shaƙi iskar ƴanci."
"Mu a ɓangaren mu na shari'a, zamu yi duk me yuwuwa a kan doka ba don ganin mafarkin mu ya zama gaskiya, ba zamu huta ba kan alƙawarin mu, ina baku tabbacin haka, gaba dai gaba dai ba zancen koma wa baya."

Yaushe aka kama Mama Biafara?

Mama Biafara, mai shekaru tsakanin 70-80, ta shiga hannun jami'an tsaro ne yayin zaman Kotun da Kanu ya halarta na ƙarshe ranar 18 ga watan Mayu, a Abuja.

Kara karanta wannan

Insha Allahu Mijina Zai Lashe Zaɓen Gwamnan Bauchi a 2023, Ministar Buhari

Matar ta kasance tamkar mahaifiyar Nnamdi Kanu tun bayan rasuwar iyayensa a shekarar 2020, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A wani labarin kuma Rundunar Yan Sanda Ta Saki Sabbin Bayanai Kan Mutanen Da Suka Kashe Deborah, Ɗalibar Da Ta Taɓa Annabi SAW

Rundunar yan sandan jihar Sakkwato ta fitar da sabon bayani kan Kes ɗin kisan Deborah Samuel, ɗalibar da ta yi batanci ga Annabi SAW.

Mai magana da yawun yan sanda, Sanusi Abubakar, ya ce sun baza komar su ta ko ina domin kama asalin makasan Deborah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: