Yan Bindiga Sun Bindige Wani Soja, Sun Sace Wani Dan Kasar Waje a Kaduna
- Wasu tsagerun 'yan bindiga sun farmaki wani kamfanin gona a jihar Kaduna sun, hallaka wani soja
- An sace wasu mutane biyu yayin da 'yan bindiga suka farmaki kamfanin gonan da ke wani yankin jihar
- 'Yan bindiga sun tasa jihohin Arewa maso Yamma a gaba, ana yawan samun tashe-tashen hankula
Kubau, jihar Kaduna - Rahoton da muke samu daga jaridar Daily Trust na cewa, wasu ‘yan bindiga sun farmaki wani kamfanin gona a garin Anchau na karamar hukumar Kubau a jihar Kaduna.
An ce tsagrun sun yi bindige wani soja tare da yin awon gaba da wasu jami’an kamfanin gonar mutum biyu da misalin karfe 1:30 na ranar Laraba.
An tattaro cewa, daya daga cikin wadanda aka sacen wani dan kasar Zimbabwe ne da ke aiki a kamfanin.
Wani dan banga da ke aiki a unguwar da abin ya faru ya ce sunan dan kasar Zimbabwe din da aka sace Mista Charles Choko.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewarsa:
“Sun kashe wani soja da ke aiki a kamfanin na gona tare da yin awon gaba da wani mutumi mai suna Charles Choko dan kasar Zimbabwe da wani Yusuf Aliyu Bello dan jihar Kano.”
Wani mutumin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa, ya ga tawagar jami’an tsaro a ranar Juma’a tana shiga dajin da ke yankin domin nemo wadanda aka sacen.
An kira shugaban karamar kukumar, Basher Suleiman Zuntu, amma ba a same shi ta waya ba. Haka nan, bai mayar da sakon tes da aka tura masa ba.
A bangarensa, DSP Mohammed Jalige, ya yi alkawarin nemo cikakken bayani kuma zai tuntubi manema labarai.
Mutum 1 Ya Mutu, 10 Sun Jikkata Sakamakon Arangama Tsakanin Mabiya Addinin Gargajiya da Kiristoci a Legas
A wani labarin, rahoton da ke fitowa daga jihar Legas ya bayyana cewa, mutum daya ya mutu yayin da 10 suka jikkata a wani artabu tsakanin mabiya addinin gargajiya da kirista.
Rundunar 'yan sandan jihar da take tabbatar da faruwar lamarin ta ce hakan ya faru a yankin Oko-Oba na jihar.
Rahotanni sun ce, an kira 'yan sanda a ranar Talata domin sanar dasu ana rikici, ana kokarin kone-kone a wurin da kiristoci ke ibada.
Asali: Legit.ng