Hamisu Wadume: An sake Sojojin Da Suka Kashe Yan Sanda, Har An Karawa Kyaftin Balarabe Girma
- Bayan shekaru biyu, yan sandan da aka kashe a Takum bayan sun kama Hamisu Wadume basu samu adalci ba
- Sabon labari na nuna cewa Kyaftin Balarabe aka ce ya jagoranci kisan yan sandan ya zama Manjo
- Kwamitin bincike da aka kafa tace bata kama Sojojin da wani laifi ba amma kuma ba'a bayyana wadanda suka kashe yan sandan ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Bayanai sun bayyana kan yadda hukumar sojin Najeriya taki hukunta Sojoji goma (10) da binciken ya nuna sun kashe jami'an yan sanda don tsiratar da wani kasurgumin dan bindiga, Hamisu Bala Wadume.
Sojojin karkashin jagoranin Kyaftin Tijjani Balarabe, sun taimakawa Wadume wajen gudu daga hannun yan sandan rundunar IRT da suka kamashi ranar 6 ga Agusta, 2019 a Takum, jihar Taraba.
Yan sanda uku da farin hula biyu suka rasa rayukansu yayinda wasu yan sanda biyar suka jikkata.
Bincike ya nuna cewa hukumar soji ta wanke wadannan sojoji daga laifin bayan zaman kwamitin 3 Batallion da aka kafa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar Punch tace wasu majiyoyi sun bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shawarin kwamitin wajen wanke sojojin daga kisan yan sandan da kuma tsiratar da mai garkuwa da mutane.
Wata majiya tace:
"3 Batallion dake Takum a jihar Taraba ta kafa kwamitin bincike kuma an kammala bincike kuma aka aikewa shugabanni."
"Daga baya sai fadar shugaban kasa ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin shugaban tsaro, Janar Olonishakin, inda aka nada Sojin kasa, na sama, na ruwa, yan sanda, DSS, lauyoyin NBA da ma'aikatar shari'a a matsayin mambobi."
"Sakamakon binciken da sukayi shine sun wanke Sojojin."
ThePunch ta rahoto cewa an samu labarin kwamitin ta gaza tabbatar da cewa Sojojin sun aikata laifin da ake zarginsu da shi.
Wata majiyar tace:
"Shugaba kasa ya amince da sakamakon kwamitin; har yanzu an karawa Kyaftin Balarabe matsyain zuwa Manjo tun Satumban 2021."
Yayinda Punch tayi kokarin ji ta bakin Kakakin hukumar Soji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya bukaci a bashi lokaci kan yayi tsokaci kan lamarin.
Amma tun ranar Litnin ya ki daukar wayarsa kuma ya ki amsa sakonni.
An Yankewa Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane Wadume Hukuncin Shekaru 7 a Magarkama
A wani labarin, babbar kotun Abuja karkashin mai shari'a Binta Kyako ta yankewa kasugumin dan bindigan da ya addabi wani yankunan jihar Taraba.
Bayan shafe lokaci ana shari'a, an kama Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume da laifukan da ake tuhumarsa, kana aka daure shi zaman shekaru bakwai a gidan yari.
Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, Wadume zai yi zaman magarkama ne tare da wasu mutane biyu da ake tuhumarsu tare.
Asali: Legit.ng