Jarumin Kwallon Kafa Ahmed Musa Da Mai Dakinsa Sun Samu Karuwar Da Namiji

Jarumin Kwallon Kafa Ahmed Musa Da Mai Dakinsa Sun Samu Karuwar Da Namiji

  • Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Ahmed Musa da matarsa sun samu karuwar 'da namiji
  • Shahararren dan wasan kwallon kafan ya bayyana sunan jinjirin a matsayin Adam Ahmed Musa (ZAYD)
  • Tuni mabiya shafinsa na soshiyal midiya suka cika sashin sharhi da sakon taya murna

Allah ya azurta Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa tare da matarsa da samun karuwar 'da namiji.

Dan wasan kwallon kafar ya je shafinsa na Instagram a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, domin sanar da wannan abun alkhairi da ya samu iyalinsa.

Ahmed Musa
Jarumin Kwallon Kafa Ahmed Musa Da Mai Dakinsa Sun Samu Karuwar Da Namiji Hoto: ahmedmusa718
Asali: Instagram

Yayin da yake hamdala ga Ubangiji a kan wannan babban kyauta da ya yi masa, dan wasan ya bayyana sunan jinjirin a matsayin Adam Ahmed Musa amma za a dunga kiransa da Zayd.

Kara karanta wannan

Bidiyoyin Shagalin Kamun Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

Ya rubuta a shafin nasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Alhamdulillah Allah ya Albar kace mu da Adam Ahmed Musa (ZAYD)❤️.”

Jama’a sun taya shi murna

Tuni masoya da abokan arziki suka cika bangaren da aka tanada don sharhi don taya shi murnar wannan babban arziki da Allah ya yi masa.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:

realalinuhu ya yi martani:

“Masha Allah, Allah ya raya Adam.”

yakubmohammed_ ya ce:

“Barka. Allah ya raya.”

real_sadeeya_kbl ta yi martani:

“Masha Allah Allah yaraya.”

madam__korede

“Masha Allah barka captain ✈️.”

zaidu_m3 ya ce:

“Allah ya raya akan Sunnah ❤️❤️.”

shehu.official ya rubuta:

“Masha Allah Allah ya raya muna ❤️.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng