'Dan Biloniya BUA Yayi Murabus Daga Kasuwancin Mahaifinsa, Kasa da Shekara 1 da Zama ED
- 'Dan biloniyan 'dan kasuwa, Abdul Samad Rabiu, ya bar kasuwancin mahaifinsa kwatsam babu zato balle tsammani
- Bayan kasa da shekara da zama darakta, Naziru Isyaku Rabiu bai bada dalilin murabus dinsa ba amma takardar tace ya bar aiki tun 17 ga Augusta
- An nada Naziru zababben daraktan BUA Foods a ranar 1 ga watan Nuwamban 2022 bayan yayi aiki matsayin mukaddashin darakta
'Dan biloniyan 'dan kasuwa, Rabiu Abdulsamad Rabiu, ya yi murabus daga matsayin zababben daraktan kamfanin BUA Foods Plc, daya daga cikin manyan kamfanonin samar da abinci a kasar nan.
Naziru ya bar kamfanin mahaifinsa tun daga ranar 17 ga watan Augustan 2022 kamar yadda takardar da kamfanin ya fitar ta bayyana.
Babu dalilin murabus dinsa na kwatsam
Matashi Naziru bai bayyana dalilinsa na yin murabus kwatsa ba. Har ila yau, wani bangare na takardar da kamfanin ta fitar ga Hukumar Tsaro da Musaya ta Najeriya tace murabus dinsa ya fara aiki daga ranar 17 ga watan Augusta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Naziru yana daya daga cikin 'ya'yan AbdulSamad Rabiu, fitaccen biloniyan 'dan kasuwa. Matashin yana da digiri a fannin tattalin arziki na kasuwanci daga jami'ar Hertfordshire.
Yana rike da matsayin zababben daraktan BUA Foods kasa da shekatra daya, kamar yadda Business Insider ta rahoto.
Tsohon ma'aikacin Seplat Petroleum
A watan Nuwamban 2021, an nada Naziru babban matsayi na zababben daraktan kamfanin BUA Foods.
Ya rike mukamai a kamfanin BUA da suka hada da daraktan kasuwanci da jami'in cigaban kasuwanci.
'Dan biloniyan yana da gogewa a kiyasin kasuwacin a Seplat Petroleum Development Company, kamfani dake kan gaba wurin harkar man fetur da iskar gas a Najeriya
N30k Kacal na Kashe: Bidiyon Siyayya Raga-raga da 'Yar Najeriya Tayi a UK ya Bada Mamaki
A wani labari na daban, wata budurwa 'yar Najeriya dake rayuwa a kasar waje mai sun Chidera Stephen, ta bayyana yawan kayan da ta siya a wani kanti a Ingila da N30,000 a wani bidiyon TikTok.
A yayin nadar bidiyon kayan, budurwar ta siya abubuwan da suka hada da fakitin naman kaji, abubuwan sha, kayan marmari da sauransu.
Fakitin fuka-fukan kaza a siye shi kasa da N2,000 karam yarra farashin ya nuna. Ya danganta da nawa ake canjin fam daya, abinda ta kashe a naira bai kai N30,000 ba.
Asali: Legit.ng