Bidiyo Yadda Magidanci Ya Kai Matarsa Mai Juna Biyu Asibiti Tare Da Janareto saboda Rashin Wutar Lantarki
- Wani magidanci ya dauki matarsa mai juna biyu tare da injin janareto zuwa asibitin Somanya a yammacin ranar Laraba, 17 ga watan Agustan 2022
- Ya tanadi janareton ne domin haskawa ma’aikatan asibitin wutar lantarki don su yi aikinsu yadda ya kamata
- Mazauna yankunan Lower Manya da Yilo Krobo suna fama da matsalar rashin wuta tsawon makonni da dama bayan kamfanin lantarki na Ghana ECG sun yanke masu wuta
Ghana – Wani magidanci da ya dauki matarsa mai juna biyu zuwa asibitin Somanya a kasar Ghana ya yi tanadi na musamman domin samawa ma’aikatan jinyan wutar lantarki don su yi aiki yadda ya kamata a kan sahibarsa.
Lamarin wanda aka nada a bidiyo ya faru ne a ranar Laraba, 17 ga watan Agusta, a yankin yammacin Ghana inda mazauna yankunan Lower Manya da Yilo Krobo ke fama da rashin wuta tsawon makonni da dama.
Yankunan sun fada cikin duhu bayan kamfanin wutar lantarki ta Ghana wato ECG ya yanke su daga kan layin wutar kasar biyo bayan wani sabani da ya shiga tsakanin ma’aikatan ECG da mazauna yankunan.
Rikicin ya barke ne a kan sauya mita da aka yi a yankunan wanda wasu mazauna suka nuna turjiya a kan shirin na saka masu mitan wuta maimakon wanda ake biya bayan an sha wuta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Mutumin ya kai janareton ne domin ma’aikatan asibitin su samu hasken lantarkin da za su yi aiki kan matarsa.
Kalli bidiyon a kasa:
Bidiyo: Magidanci Ya Ki Karbar Nama Yanka 2 Da Matarsa Ta Bashi, Ya Shiga Madafi Ya Diba Da Kansa
A wani labarin, bidiyon wani magidanci yana yiwa matarsa korafi a kan basa yankan nama biyu kacal a kodayaushe ya baiwa mutane da dama dariya sannan ya haifar da martani sosai a soshiyal midiya.
Hotuna: Dan Maiduguri Ya Kera Adaidaita Mai Aiki Da Lantarki Wanda Ka Iya Gudun 120Km Bayan Chajin Minti 30
A cikin bidiyon wanda shafin @instablog9ja ya wallafa a Twitter, mutumin ya bayyana cewa shine yake fita samo kudaden da ake kashewa don haka ya cancanci ayi masa karin nama a abinci.
Mutumin wanda ya fusata matuka ya tsawatarwa matarsa sosai yayin da ya shiga madafi da kansa sannan ya zubawa kansa abinci da hannunsa ba tare da bata lokaci ba.
Asali: Legit.ng