A Yi Amfani Da 'Kudin Abacha' Don Warware Matsalar ASUU, In Ji Dan Majalisar Najeriya

A Yi Amfani Da 'Kudin Abacha' Don Warware Matsalar ASUU, In Ji Dan Majalisar Najeriya

  • Dan Majalisar Wakilai na tarayya, Dachung Musa Bagos ya bada shawaran a biya wa ASUU bukatarsu da kudin Abacha da aka kwato
  • Musa Bagos ya ce bangaren zartarwa ne kadai ta ke gaban kanta da kudin ba tare da tuntubar majalisar tarayya ba sai da suji an fitar da kudi don wani aiki
  • Dan majalisar mai wakiltar Jos South da Jos East ya yi korafin cewa ana kashe kudin ne wurin wasu ayyukan da ba su kai batun ilimin jami'o'in muhimmanci ba a yanzu

Dachung Musa Bagos, dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar Jos South/Jos East, ya ce a yi amfani da Dalla miliyan 23 cikin kudin aka zargin Abacha ya sace a biya wa kungiyar ASUU bukatunta.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Fusata, Ya Bada Umurnin Abin Da Za A Yi Wa Sojan Da Ya Kashe Sheikh Goni Aisami

Dan majalisar ya yi magana ne a hirar da aka yi da shi a Channels Television a ranar Laraba, The Cable ta rahoto.

Yajin Aikin ASUU
A Yi Amfani Da 'Kudin Abacha' Don Warware Matsalar ASUU, In Ji Dan Majalisar Najeriya. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar Talata, gwamnatin tarayya da gwamnatin Amurka sun cimma yarjejeniyar dawo da sabbin kudaden da ake zargin tsohon shugaban mulkin soja Sani Abacha ya wawure.

Abubakar Malami, ministan shari'a kuma antoni janar ya ce za a yi amfani da kudin da aka yi wa lakabi da 'Abacha 5' don karasa ginin titin Abuja-Kano, Legas-Ibadan da Gadar Second Niger.

Masu zartarwa ba su tuntubar mu kafin kashe kudin da aka kwato, Bagos

Da ya ke martani kan lamarin, Bagos yace gwamnatin tarayya bata aiki tare da majalisar tarayya wurin rabon kudin da aka karbo.

Wani sashin kalamansa:

"Wannan shine shekara ta ta uku a majalisar, ba mu taba tattauna yadda za a raba kudin da aka kwato ba. Sai dai mu ji gwamnati ta kwato kudi ta ware kudin don wasu ayyuka da ta ke so.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Buhari ya yi Allah wadai da kisan gillan da aka yiwa Shehin Malami a Yobe

"Muna da abubuwan da suke damun kasa. A yanzu, ASUU ta dade tana yajin aiki kuma gwamnati na kokarin magance matsalar.
"A matsayi na na wakilin mutane, Idan zan fada abin da za a yi da kudin, zan ce, mai zai hana a biya wa ASUU bukatunta saboda mafi yawancin matasa da ke gida su koma makaranta?".

Dan majalisar ya cigaba da cewa baya tsammanin abubuwan da gwamnatin ke kashe kudi a kai sune mafi muhimmanci a yanzu.

An shiga wata bakwai na yajin aikin a yanzu kuma babu tabbacin lokacin da za a janye bayan zaman sulhu da dama amma ba a cimma matsaya ba.

Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

A wani rahoton, Gwamnan Jihar Ebonyi David Umahi ya ce ilimin Jami'a fa ba na kowa da kowa bane, rahoton The Punch.

Umahi ya jadada cewa ba adalci bane a yi tsammanin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ciyo bashin fiye da Naira tiriliyan 1 don biyan bukatun ASUU.

Kara karanta wannan

Taron NBA: Abin da Atiku, Obi suka fada, yayin da aka nemi Kwankwaso aka rasa

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne kan yajin aikin da malaman jami'o'i ke yi, a lokacin da ya karbi bakuncin tawaga daga asusun yan sandan Najeriya karkashin jagorancin Dr Ben Akabueze, a Abakaliki a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164