DMO: Zunzurutun Bashin da Ake Bin Najeriya Ya Zarta Kudin Shiga da Take Samu

DMO: Zunzurutun Bashin da Ake Bin Najeriya Ya Zarta Kudin Shiga da Take Samu

  • Zunzurutun basin da ake bin Najeriya a halin yanzu ya zarce kudin shigar da kasar ke samu kamar yadda Ofishin Kula da Basussuka ya bayyana
  • Darakta Janar ta Ofishin DMO, Patience Oniha, tace yawan kudaden da ake biyan basi ya tasi har ya kai 109%
  • Daga watan Disamban shekarar da ta gabata zuwa Maris na wannan shekarar, Najeriya ta biya N3.83 tiriliyan na bashi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Najeriya ta kashe kudade masu yawa wurin biyan bashi fiye da wanda take samu tsakanin watan Janairu zuwa Afirilu na wannan shekarar inda darakta janar na Ofishin Kula da Basusska, Patience Oniha.

Yawan kudin da ake amfani da shi wurin biyan bashi ya zama abun damuwa ga gwamnatin tarayya saboda a watanni hudu na farkon shekarar nan ta biya bashi da sama da kudin shigar da take samu.

Kara karanta wannan

2023: Sarkin Kano Sanusi ya ba 'yan Najeriya shawarin shugaban da za su zaba

Darakta janar din ta kara da cewa, yawan kudaden da ake biyan bashi ya karu da kashi 109 tsakanin watan Disamban shekarar da ta gabata da na Maris din wannan shekarar, daga N429 biliyan da N896 biliyan.

DMO Nigeria
DMO: Zunzurutun Bashin da Ake Bin Najeriya Ya Zarta Kudin Shiga da Take Samu. Hoto daga @thenation
Asali: Twitter

The Nation ta rahoto cewa, kamar yadda bayanan da ofishin kula da basukan suka bayyana, an kashe N3.83 tiriliyan wurin biyan bashi a kasar nan cikin watanni 15.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oniha ta sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jiya cewa, "yawan aron da ake yi ana hada shi da tsarikan aron kudi

"Duk da a bayyane yake, daya daga cikin abubuwan da kwarraru ke cirewa cikin kiyasin shine sabon salon rancen na nufin karin yawan bashin da kuma bashin da za a biya nan gaba," tace yayin da take bayyana cewa, Najeriya na bukatar karin kudin shiga da kula da basukan da ake bin ta yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Hotuna da Bidiyon shagalin Kamun diyar Sanata Sahabi Yau sun Dauka Hankali

Zamfara: Kwamitin Yakar 'Yan Bindiga Ya Gindaya wa Turji Sharadin Tuba

A wani labari na daban, Kwamitin jihar Zamfara na gurfanar da laifukan da suka shafi 'yan bindiga sun ce har sai Bello Turji, fitaccen shugaban 'yan bindiga ya fito bainar jama'a ya mika makamansa tare da sanar da tubansa, ba za a karba tubansa a matsayin sahihiya ba.

Shugaban kwamitin, Abdullahi Shinkafi, ya sanar da hakan a jawabin da yayi ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, Channels TV ta ruwaito.

Shinkafi wanda ya fito daga karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, inda Turji ke yawaita barnarsa, yace kusan watanni shida kenan babu labarin farmakin 'yan ta'adda ko sace mutane da aka saba a yankin da kananan hukumomin Zurmi, Isa da Sabon-Birni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng