Kyakkyawar Budurwa Mai Digiri ta Koma Siyar da Kayan Miya, Bidiyo Ya ba Jama'a Mamaki
- Wata kyakyawar budurwa da ta kammala digirinta a fannin kimiyyar ruwa ta bayyana cewa yanzu ta zama 'yar kasuwa
- Budurwar ta bayyana a bidiyo cike da murmushi inda take zubawa kwastoma kayan miya duk da digirin da take da shi
- Wasu jama'a sun yi martani kan bidiyon inda suka bayyana cewa akwai mutane da yawa dake fuskantar irin abinda take fuskanta
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Wata matashiyar budurwa wacce ta kammala digiri a fannin kimiyyar ruwa ta shiga gasar TikTok inda mutane ke bayyana abinda suka karanta a makaranta da kuma sana'ar da suka koma daga baya.
A bidiyon da ta wallafa, an ga budurwar tana murmushi sanye da rigar kammala digiri yayin da ta karkace tana daukar hoto da mahaifiyarta.

Asali: UGC
Mai digiri ta koma 'yar kasuwa
Wani bidiyonta kuwa ya nuna kyakyawar budurwar da ta kammala digirin tana siyar da kayan gwari kamarsu albasa, tumatir da sauransu a kasuwa.

Kara karanta wannan
So Nake su Koyi Sana'a da Tattali: Mata Mai Gidan Gona ta ba Yaranta Aiki, Albashinsu 105k a Sati
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kasuwar, budurwar ta bayyana sanye da gilashi yayin da take cigaba da murmushi yayin da take zuba kayan miya cikin leda.
Jama'a sun yi martani
A yayin rubuta wannan rahoto, bidiyon ya tara sama da tsokaci 300 tare da jinjina sama da 27,000.
Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin martanin.
user3232987758582 yace:
"A kalla kin yi kyau da kike sana'ar."
Brian_thomas yace:
"Ga mutanen dake karanta kimiyyar ruwa, kada ku damu. Kowa yana da labarinsa mabanbanci. Ni a bangarena, na samu aiki tun kafin in kammala karatuna."
ODZZ yace:
"Abun sha'awar shi ne kina bayyana halin da kike ciki har sai komai ya daidaita."
Javan Matamano yace:
"Ki yarda da Ubangiji, lokaci na zuwa. Ubangiji yayi miki albarka."
Sana'a da Tattali: Mata Mai Gidan Gona ta ba Yaranta Aiki, Albashinsu 105k a Sati

Kara karanta wannan
Ya Rabu Dani Saboda Ina Da Muni: Hotunan Sauyawar Wata Budurwa Shekaru Bayan Saurayi Ya Guje Ta Ya Ba Da Mamaki
A wani labari na daban, Kimoi Jerotich, wata mata mai yara uku ta bai wa jama'a mamaki bayan wasikar daukar aikin da tayi wa yaranta biyu ta bayyana.
A wasikar da ta yadu a soshiyal midiya, Jerotich ta dauka Shawn mai shekaru shida da Ryan mai shekaru tara aikin shekaru uku kacal.
A yayin tattaunawa da kafar yada labaran Kenya ta Tuko.co.ke, HRM tayi bayanin cewa ta yanke wannan hukuncin ne saboda tana son shirya yaranta saboda gaba da wuri.
Asali: Legit.ng