NDLEA ta Cafke Basaraken Arewa da Hodar Iblis da Miyagun Kwayoyi
- Hukumar NDLEA reshen jihar Sokoto ta kama dagacin kauyen Ruga dake Shagari da hodar Iblis da kwayoyin Diezepam
- Kwamandan rundunar, Adamu Iro, yace basaraken ya amsa laifinsa kuma yace ya dade yana safarar miyagun kwayoyi
- An kama dagacin da 436.381kg na tabar wiwi da 1kg na kwayar Diazepam a gidansa sakamakon samamen da jami'ai suka kai
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Sokoto - Hukumar Yaki da Fasa-Kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA, reshen jihar Sokoto, ta damke wani da ake zarginsa da dillancin miyagun kwayoyi mai suna Umar Mohammed, dagacin kauyen Ruga dake karamar hukumar Shagari.
A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Talata, 23 ga watan Augusta, kwamandan NDLEA na jihar, Adamu Iro, yace wanda ake zargin ya shiga hannu ne sakamakon bayanan sirri da hukumar ta samu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya rahoto, Iro yace wanda ake zargin basarake ne kuma sunansa ya dade a cikin jerin wadanda hukumar ke zargi na tsawon lokaci.
"Da farko matarsa muka fara kamawa da miyagun kwayoyi masu yawa amma sai muka saketa bayan bincike ya nuna cewa na mijinta ne.
"Toh Alhamdulillah, a ranar Litinin mun yi nasarar kama mutumin da 436.381kg na tabar wiwi da 1kg na kwayar Diazepam a gidansa," Iro yace.
Kwamandan ya kara da cewa, wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma ya tabbatarwa da hukumar cewa ya dade yana kasuwancin nan na tsawon lokaci.
Yace hukumar zata tabbata da an yi bincike mai kyau kuma cikin sauri domin mika wanda ake zargin gaban kotu, Daily Trust suka rahoto.
Iro ya kara da tabbatarwa da 'yan kasa burin NDLEA na kai samame mafakar masu safarar kwayoyi kuma ta gurfanar dasu yadda ya dace.
Ya yi kira ga jama'a da su goyi bayan hukumar ta hanyar da zata tabbatar da kawo karshen duk wani nau'i na amfani da miyagun kwayoyi a al'umma.
Zamfara: Kwamitin Yakar 'Yan Bindiga Ya Gindaya wa Turji Sharadin Tuba
A wani labari na daban, Kwamitin jihar Zamfara na gurfanar da laifukan da suka shafi 'yan bindiga sun ce har sai Bello Turji, fitaccen shugaban 'yan bindiga ya fito bainar jama'a ya mika makamansa tare da sanar da tubansa, ba za a karba tubansa a matsayin sahihiya ba.
Shugaban kwamitin, Abdullahi Shinkafi, ya sanar da hakan a jawabin da yayi ga manema labarai a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, Channels TV ta ruwaito.
Shinkafi wanda ya fito daga karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, inda Turji ke yawaita barnarsa, yace kusan watanni shida kenan babu labarin farmakin 'yan ta'adda ko sace mutane da aka saba a yankin da kananan hukumomin Zurmi, Isa da Sabon-Birni.
Asali: Legit.ng