Hukumar Yan Sanda Zata Baiwa Matasa 3000 Horo Don Bada Tsaro A Jihar Katsina
- Saboda rashin isassun yan sanda a Katsina, gwamnatin jihar ta fara shirin horar da matasa majiya karfi
- Hadimin Masari ya ce mutum 3000 zasu horar kuma su turasu faggen fama don samar da tsaro
- Jihar Katsina na cikin jihohin Arewa maso yamman dake fama da matsalar tsaro
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Hukumar yan sandan Najeriya na shirin baiwa matasa majiya karfi 3000 horo na musamman don su taimakawa jami'anta wajen tabbatar da tsaro a jihar Kastina.
Mai baiwa gwamna Aminu Masari shawara kan harkokin tsaro, Ahmed Katsina, ya bayyana hakan ranar Alhamis, rahoton Punch.
Ya bayyana cewa tuni an kammala horar da mutum 500 kuma an turasu kananan hukumomin dake fuskantar matsaloli na tsaro.
Ya kara da cewa za'a kara horar da wasu matasan 600 kuma a turasu faggen fama nan ba da dadewa ba.
A cewarsa:
"Manufarmu itace samun horarrun matasa 3,000 da zasu taimakawa jami'an tsaro a jihar. Zamu tura mutum 88 kowace karamar hukuma."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Tuni Mun horar da 500 a ofishin yan sandan Mopol kuma an turasu faggen fama."
"A karshe zamu tura matasa 3,000 kananan hukumomi 34 na jihar. Wannan na cikin wani shiri na bai-uku da ake kafa don dakile matsalar tsaro musamman ta'addanci a jihar."
Yallabai ba kada isasshen jami'an da zasu iya samar da tsaro a Katsina, Masari ga IGP Alkali
A bara, Gwaman jihar Katsina, Aminu Bello Masari, yace hukumar yan sanda ba tada isasshen jami'an da zasu samar da tsaro kan jiha mai adadin mutane milyan takwas.
Masari ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin Sifeto Janar na yan sanda, Alkali Usman Baba, a gidan gwamnatin jihar
Masari yace babu isassun yan sandan da zasu iya bada tsaro a jihar Kastina.
Asali: Legit.ng